Mataimakin Shugaban kasa Osinbajo ya gargadi Kamfanin wutan Najeriya

Mataimakin Shugaban kasa Osinbajo ya gargadi Kamfanin wutan Najeriya

- Farfesa Yemi Osinbajo ya gargadi Kamfanin wutan lantarkin Najeriya

- Yemi Osibanjo yace idan ba za su iya kasuwanci ba su saida kamfanin

- Gwamnati ta saidawa 'Yan kasuwa wutar lantarki amma har yanzu da sake

Mun samun labari daga Jaridar Daily Trust cewa Mataimakin Shugaban kasa Yemi Osinbajo ya nuna Kamfanin lantarki Najeriya da dan yatsa. Osinbajo ya gargadi Kamfanin wutar kasar cewa su saida Kamfanin idan ba za su iya gudanar da kasuwanci ba.

Mataimakin Shugaban kasa Osinbajo ya gargadi Kamfanin wutan Najeriya

Mataimakin Shugaban kasa Farfesa Osinbajo

Farfesa Osinbajo ya ja kunnen Kamfanin wutan lantarkin ne a wani taro da ake yi a Abuja bayan da Shugaban Kamfanin Heirs Holding Limited watau Tony Elumelu ya kira Gwamnati ta kara sa kudi a cikin Kamfanin raba lantarki na kasar watau DISCOS.

KU KARANTA: Wata Kungiya a Amurka ta gargadi Shugaba Buhari

Mataimakin Shugaban kasar yace da su idan ba za su iya rike Kamfanin wutan ba su saida Kamfanin su cire hannun su a ciki. Osinbajo yace Gwamnati ba ta da wannan kudin sai dai Kamfanin su nemi hanyar samun kudi da kan su,

Gwamnatin Tarayya ta saidawa 'Yan kasuwa kashi 60% na Kamfanin raba wutar lantarki a Kasar amma har yanzu ba a ga wani amfani ba na kirki idan aka kamanta.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Dandalin Kannywood: Atiku ne kadai ke da mabudin gyaran Najeriya - Fati Muhammad

Dandalin Kannywood: Atiku ne kadai ke da mabudin gyaran Najeriya - Fati Muhammad

Dandalin Kannywood: Atiku ne kadai ke da mabudin gyaran Najeriya - Fati Muhammad
NAIJ.com
Mailfire view pixel