Buhari ne ya bani damar aiki da Naira Biliyan 640 yayin da yake kasar Landan - Baru

Buhari ne ya bani damar aiki da Naira Biliyan 640 yayin da yake kasar Landan - Baru

A wani sabon rahoto da NAIJ.com ta samu ya bayyana cewa, shugaban kasa Muhammadu Buhari ne ya bayar da izinin gudanar da aikace-aikacen kamfanin NNPC a lokacin da yake kasar Landan yayin duba lafiyarsa.

Shugaban kamfanin Mista Maikanti Baru ne ya bayyana hakan, inda ya ce shugaba Buhari ne ya ba shi izinin amfani da Dalar Amurka Biliyan 1 a ranar 10 ga watan Yuli, da kuma Dalar Amurka Miliyan 780 a ranar 31 ga watan Yuli na shekarar nan wajen gudanar da wasu aikace-aikace na kamfanin.

Marubuta da dama da masu ruwa da tsaki sun yi korafin cewa, shugaba Buhari bai cancanci bayar da wannan izini ba, domin kuwa ba shi da hurumin bayar da shi tun da har ya riga da ya dora shugabancin kasar nan a hannun mataimakin sa Farfesa Osinbajo.

Buhari ne ya bani damar aiki da Naira Biliyan 640 yayin da yake kasar Landan - Baru

Buhari ne ya bani damar aiki da Naira Biliyan 640 yayin da yake kasar Landan - Baru

Tun a ranar 9 ga watan Mayu na shekarar nan, shugaba Buhari ya yi wata rubutacciyar wasika zuwa ga shugabannin majalisun dattijai da wakilai, inda ya ya bayyana musu wakilcin shugabancin kasar nan a hannun mataimakinsa Osinbajo.

KARANTA KUMA: Gargadi na marmaza: Buhari ya janye dakarun soji daga Kudu maso Gabas - Wata kungiyar kare hakkin dan Adam

A ranar 21 ga watan Agusta, shugaban kasar ya sake rubutawa majalisun biyu cewa zai ci gaba da shugabantar kasar nan daga ranar Litinin din da ta yi daidai da 21 ga watan Agusta na shekarar 2017.

A ranar Litinin din da ta gabata ne, Mista Baru ya fayyace zare da abawa akan cewar yayi amfani da wannan makudan kudin ne sakamakon izini da ya samu daga wajen shugaban kasa, wanda a kwanaki kadan da suka gabata, an yiwa kamfanin ca a kai domin jin yadda kudi suke sulalewa ba tare da bayan dalilin inda suka shiga ba.

Domin shawara ko bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Abin da Shugaba Buhari ya fadawa ‘Yan APC na Kasar Inyamurai a Villa

Abin da Shugaba Buhari ya fadawa ‘Yan APC na Kasar Inyamurai a Villa

Abin da Shugaba Buhari ya fadawa ‘Yan APC na Kasar Inyamurai a Villa
NAIJ.com
Mailfire view pixel