An kashe wani dan Najeriya mai shekaru 25 a kasar Afirika ta Kudu

An kashe wani dan Najeriya mai shekaru 25 a kasar Afirika ta Kudu

- An kashe wani dan Najeriya mai shekaru 25 a kasar Afirika ta Kudu

- Jakadan Najeriya a can kasar ne ya tabbatar da hakan

- Wannan kisa ya tunzura 'Yan Najeriya mazauna Afirika ta kudu amma Jakadun Najeria sun umurce su da su zauna lafiya

Ko mako daya bai shude ba da kashe Mista Jeleli Omoyele wanda dan Najeriya ne mazaunin kasar Afirika ta Kudu, wanda ke sana'ar gyaran wayar hannu, mai shekara 35, sai gashi an sake kashe wani matashin dan Najeriya a can kasar Afirika ta Kudu.

Sunan matashin Mista Ibrahim Olalekan Badmus, mai shekaru 25 kuma dan asalin Jihar Legas. Babban Jakadab Najeriya a can kasar ne ya tabbatar da kisan.

Babban Jakadan Najeriya a can Afrika ta kudu Mista Godwin Adama, ya tabbatar wa NAN ta wayar tarho, bisa bayanai da su ka samu, ana zargin dan sandan kasar ne ya kashe Badmus a ranar Talata ne.

DUBA WANNAN: Buhari yaci amanar musulmai bisa nadin Aisha Ahmad a CBN

Wannan kisa ya tunzura 'yan Najeriya mazauna kasar amma Jakadun sun samu nasarar shawo kan su. Sun kuma umurce su da su kasance masu bin doka da oda.

Jakadun sun tuntubi hukumar 'yan sanda na yankin da abun ya faru a inda suka tabbatar masu cewan zasu gudanar da bincike don bin diddigin wannan mummunar al'amari.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Ashe Iran ke baiwa 'yan tawayen Yemen makaman yaki

Ashe Iran ke baiwa 'yan tawayen Yemen makaman yaki

Ta tabbata' Kasar Iran ke taimakawa 'yan tawayen Kasar Yemen
NAIJ.com
Mailfire view pixel