An kashe dan Najeriya mai shekaru 25 a kasar Afrika ta Kudu

An kashe dan Najeriya mai shekaru 25 a kasar Afrika ta Kudu

- An kara kashe wani dan Najeriya mai shekaru 25 a kasar Afrika ta Kudu

- Jam'i'in yansadar kasar Afrika ta Kudu ake zargi da kashe dan Najeriya

- Jakadan Najeriya dake a kasar Afrika ta Kuduya bukaci yan Najeriya su zama masu bin doka da oda

Kungiyar yan Najeriya dake Afrika ta Kudu sun tabbatar da kashe wani dan Najeriya kasar Afrika ta Kudu mai sunnna, Mitsa Ibrahim Olalekan Badmus, mai shekaru 25 daga jihar Legas.

Wannan kisan ya zo ne mako daya bayan harbe wani dan Najeriya mai gyaran wayan tarho, Mitsa Jelili Omoyele, mai shekaru 35 a Doornfentein kusa da Johannesburg.

Mista Godwin Adama, jakadan Najeriya a kasar Afrika ta kudu, ya fada ma yan jarida News Agency of Nigeria (NAN) a wayar tarho cewa an kashe Badmus ne ranar Talata a garinVaal Vreneging kusa da babban birnin kasar Johannesburg.

An kashe dan Najeriya mai shekaru 25 a kasar Afrika ta Kudu

An kashe dan Najeriya mai shekaru 25 a kasar Afrika ta Kudu

Ya ce rahoton da suka samu ya nuna “Dansadar kasa Afrika ta Kudu ya kashe mamamcin."

KU KARANTA : Rikicin Rivas : Yawan mutanen da suka mutu ya karu zuwa 25

Adama ya ce, “ya ziyarci ofishin rundunar yansandar unguwar da abun ya faru tare da wasu yan Najeriya mazauna kasar dan sannin ainihin abun da ya faru. Yansanda sunyi alkawarin bayyana abun da ya faru bayan sun kamala bincike."

“Wasu jami’an yansanda na musamman za su yi binciken,” Inji shi.

Adama ya bukaci al’ummar Najeriya dake zama kasar da su kwanatar da hankalin su hukuma ta na binciken al’amarin, kuma su zama ma su bin doka da oda.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Ta tabbata' Kasar Iran ke taimakawa 'yan tawayen Kasar Yemen

Ta tabbata' Kasar Iran ke taimakawa 'yan tawayen Kasar Yemen

Ta tabbata' Kasar Iran ke taimakawa 'yan tawayen Kasar Yemen
NAIJ.com
Mailfire view pixel