Alheri gadon barci: Sarkin Gombe ya samar ma matasa 28 aikin Soja da Ɗansanda (Hotuna)

Alheri gadon barci: Sarkin Gombe ya samar ma matasa 28 aikin Soja da Ɗansanda (Hotuna)

- Sarkin Gombe Abubakar Shehu ya samar ma matasa 28 aikin damara

- Matasan sun hada da Yansanda 10 da Sojoji 18

Sau dayawa ana yi ma manyan Arewa da su dinga taimaka ma matasa da aikin yi, tallafin karatu, ko kuma jarin kasuwanci, domin hakan zai rage zaman banza da kuma rage barazana ga tsaro.

Sai dai a lokacin da wasu manyan ke yin watsi da wannan kiraye kiraye, wasu kuwa, rungumarsa suke yi, don kuwa a nan, an samu wasu matasa su 28 da Mai Martaba Sarkin Gombe, Alhaji Abubakar Shehu Abubakar III ya samar ma aikin yi.

KU KARANTA: Wasu matasa a Kano sun jefe wani mutumi mai shekaru 70 har lahira

Alheri gadon barci: Sarkin Gombe ya samar ma matasa 28 aikin Soja da Ɗansanda (Hotuna)
Alheri gadon barci: Sarkin Gombe

Jaridar Rariya ta ruwaito bababn jami’in kula da sadar na fadar Sarki, Muhammad Bappah Idaya yace goma sha takwas daga cikin matasan sun samu aikin Soja ne, yayinda goma daga cikinsu suka samu aikin Dansanda, kuma dukkaninsu mai martaba ne ya sama musu ayyukan.

Alheri gadon barci: Sarkin Gombe ya samar ma matasa 28 aikin Soja da Ɗansanda (Hotuna)
Sarkin Gombe

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Sarkin ya tarbi matasan yayind a suka kawo masa ziyarar godiya da ban girma har fadarsa dake garin Gombe, bugu da kari sun bayyana godiyarsu, inda suka bukaci Sarkin ya cigaba da yin wannana aikin alheri.

Alheri gadon barci: Sarkin Gombe ya samar ma matasa 28 aikin Soja da Ɗansanda (Hotuna)
Yansandan da Sojoji

Daga karshe sun taya Sarkin da addu’ar karin lafiya, da tsawon kwana mai albarka, Allah ya kara ma sarkiya lafiya da imani. Idan ba'a manta ba a kwanakin baya ma Sarkin na Gombe ya dauki nauyin karatun wasu daliban Firamari da yawansu ya hauwa 1000.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Me zaka ce game da Yansandan Najeriya, kalla a Legit.ng TV

Asali: Legit.ng

Online view pixel