Labaran Kannywood: An karrama jaruman Kannywood da kyautuka a Abuja

Labaran Kannywood: An karrama jaruman Kannywood da kyautuka a Abuja

Mashirya bikin karrama jaruman Fina finan Kannywood da suka taka rawar gani na City People Award sun sake shirywa wata gagarumar biki, inda suka karrama yan Fim da dama.

Kannywood Scene ta ruwaito fitaccen jarumin fina finan Hausa, kuma wanda ya dade ana damawa da shi, wato Ali Nuhu, wanda aka fi sani da suna Sarkin Kannywood, shine ya fi haskawa a daren bikin.

KU KARANTA: Wake ɗaya shi ke bata miya: Asirin wasu Ýansanda 2 da Sojan ruwa 1 masu satar mutane ya tonu

Labaran Kannywood: An karrama jaruman Kannywood da kyautuka a Abuja

Ali Nuhu

Jarumi Ali Nuhu ya lashe kyautar dan Fim din da ya fi samun nasarori a cikin kafatanin masu harkar Fim gaba daya, wato ‘Life Time Achivement Award’, kamar yadda majiyar NAIJ.com ta ruwaito.

Labaran Kannywood: An karrama jaruman Kannywood da kyautuka a Abuja

Rashida

Shima Aminu Shariff Momoh ba’a barsa a baya ba, inda ya lashe kyautar gwarzon dan Fim, yayin da Lawal Ahmad ya lashi kyautar Mai mara ma gwarzo baya, sai Kamal Alkali ya lashe kyautar Daraktan Fim masi hazaka.

Labaran Kannywood: An karrama jaruman Kannywood da kyautuka a Abuja

Jarumai

Sauran sun hada da Umar M Sheriff daya lashe kyautar gwarzon Fim mai tasowa, yayin da Rashin Laddo ta tafi gida da kyautar Zakakurar Fim, sai kuma Maryam Aliyu, wanda ta lashe kyautar Zakakurar yar Fim mai tasowa, da kuma Hajara Isah wanda ita ta samu kyautar karramawa a yayin bikin.

Labaran Kannywood: An karrama jaruman Kannywood da kyautuka a Abuja

Jarumai

A yayin jawabinsa, Umar M Sheriff yace ya sadaukar da kyautar daya samu zuwa ga gwarzon sa, kuma Maigidansa Ali Nuhu, inda ya mai komai a harkar Fim.

Kalli bidiyon a nan:

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.naij.com

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Ta tabbata' Kasar Iran ke taimakawa 'yan tawayen Kasar Yemen

Ta tabbata' Kasar Iran ke taimakawa 'yan tawayen Kasar Yemen

Ta tabbata' Kasar Iran ke taimakawa 'yan tawayen Kasar Yemen
NAIJ.com
Mailfire view pixel