Ilimi ya shiga mawuyacin hali a jihar Kaduna: Kalli jarabawar da Malaman firamari suka gagara masawa

Ilimi ya shiga mawuyacin hali a jihar Kaduna: Kalli jarabawar da Malaman firamari suka gagara masawa

- Malamai 21,000 sun fadi jarabawan daliban aji 4 na Firamari a jihar Kaduna

- Gwamnan jihar Kaduna yace zasu sallami malaman, kuma su maye gurbinsu da sabbi

Biyo bayan cece kuce daya dabaibaye maganan da gwamnan jihar Kaduna Malam Nasiru El-Rufai yayi na cewa za’a sallami Malamai 21,000 daga jihar saboda sun gagara cin jarabawar yan aji 4, NAIJ.com ta yi bincike.

Binciken da muka yi kuwa ya kai mu ga zakulo tambayoyin da aka yi ma Malaman nan, inda muka samu tambayoyin daga wani ma’abocin shafin Facebook, Bashir Ibrahim Dabo.

KU KARANTA: Daga Kannywood: Maryam Booth ta zazzaga ma Saurayinta kalaman Soyayya

Wasu daga cikin tambayoyin an bukaci Malaman su ba fadi wanene gwamnan jihar Kaduna, wanene kwamishinan Ilimin jihar Kaduna, wanene ministan Ilimi, wanene shugaban hukumar ilimi ta bai daya na jihar Kaduna, SUBEB, wanene shugaban kasar Amurka, da kuma me UBEC ke nu fi?

Ilimi ya shiga mawuyacin hali a jihar Kaduna: Kalli jarabawar da Malaman firamari suka gagara masawa

Takardar jarabawar

A bangaren lissafi an tambayi Malaman tambayoyi guda 10, yayin da a bangaren Ilimin zamantakewa aka tambaye su amsa tambayoyi 5 da suka hada da wasu cututtuka ne ke damun jama’an su, menene hakkin iyaye akan yayansu, na’urorin sadarwar zamani guda 3 da sauransu.

Ilimi ya shiga mawuyacin hali a jihar Kaduna: Kalli jarabawar da Malaman firamari suka gagara masawa

Jarabawar

Jarabawar ta kare da tambayar Malaman tambayoyi da suka shafi bangaren koyarwar kansa, inda aka bukaci da suyi bayani akan abubuwan da koyar da dalibai ya kunsa.

Ilimi ya shiga mawuyacin hali a jihar Kaduna: Kalli jarabawar da Malaman firamari suka gagara masawa

Jarabawar

Gwamnatin jihar Kaduna ta shirya jarabawar ne da nufin gwada Malaman don tabbatar da sun san abin da suke yi ma daliban su, haka ne ya sa aka basu tambayoyin yan aji 4, kuma aka bukaci da kowannensu ya samu kashi 75 cikin 100, amma sai ga shi sama da 20,000 sun gaza.

Ilimi ya shiga mawuyacin hali a jihar Kaduna: Kalli jarabawar da Malaman firamari suka gagara masawa

Jarabwar

Hakan ta sanya gwamnatin yanke shawarar sallamar Malaman da suka fadi jarabawar, inda zasu dauki sabbin Malamai don su maye gurbin su.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.naij.com

Barnar da ruwa yayi, kalla a NAIJ.com TV

Source: Hausa.naija.ng

Related news
An fara samun sauki a gidajen man fetur da ke birnin tarayya, Abuja

An fara samun sauki a gidajen man fetur da ke birnin tarayya, Abuja

Layin man fetur da ta kuno kai a Abuja ta fara raguwa sosai a halin yanzu
NAIJ.com
Mailfire view pixel