Wani Dalibi makaho Dan baiwa da yayi karatu a Jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya

Wani Dalibi makaho Dan baiwa da yayi karatu a Jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya

– Ga wani Makaho dan baiwa da yayi karatu a Jami’ar A.B.U Zariya

– Wannan Dalibi ko da Makaho ne yana cikin zakakurai a ajin su

– Sunan wannan Bawan Allah Usman ya kuma kammala karatun Digiri

Mun samu labari cewa wani makaho ya kammala Digiri a Jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya da maki mai tsoka a yanzu haka.

Wani Dalibi makaho Dan baiwa da yayi karatu a Jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya
Usman dai makaho ne kuma yayi karatu a Ahmadu Bello ta Zariya

Ga wani Bawan Allah dan baiwa mai Usman wanda makaho ne kuma zakakuri a ajin sa. Usman ya kammala karatun sa na Digiri yanzu haka a Jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya a fannin aikin jarida da kafofin yada labarai.

KU KARANTA: Dan wasan Najeriya Ahmed Musa a gidan mai

Wani Malamin sa mai suna Muhammad Hashim Suleiman ya bayyana cewa Usman yana cikin hazikan da ke ajin sa asali ma ya kammala karatun na sa ne da mataki mai tsoka. Usman dai ya san muryar kowane Malamin sa ko da ba ya iya ganin su.

Usman yana aiki ne da wata na’ura ta makafi wajen karatu Inji Malamin sa. Usman kuma Musulmi ne mai kishin addinin sa kuma babban Aminin sa wani Kirista ne mai suna Silas tun farkon shigowar sa Jami’a kuma yanzu haka yana soyayya da wata yarinya. 

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel