Russia 2018: Kasar Argentina da Portugal sun samu zuwa Gasar Duniya

Russia 2018: Kasar Argentina da Portugal sun samu zuwa Gasar Duniya

- Kasar Argentina da Portugal sun isa Gasar cin kofin Duniya na 2018

- Sai a ranar wasan karshe manyan kasashen su ka samu isa Gasar

- Sauran Kasashen Duniya irin su Faransa sun samu shiga sahun Gasar

A fagen wasan kwallon kafa za ku ji cewa Kasar Argentina da Portugal sun samu zuwa Gasar cin kofin Duniya na World Cup shekarar badi.

Russia 2018: Kasar Argentina da Portugal sun samu zuwa Gasar Duniya

Lionel Messi ya samu zuwa Gasar cin kofin Duniya

Kasar Portugal ta doke Switzerland da ci 2-0 wanda ke nufin Dan wasa Cristiano Ronaldo da kasar sa za su samu zuwa Gasar na World Cup a badi. Haka kuma Kasar Argentina ta casa Ecuador da ci 3-1 inda Dan wasa Lionel Messi ya rufawa Kasar sa asiri.

KU KARANTA: Dan wasan Super Eagles ya samu mukudan kyauta bayan wani wasa

Russia 2018: Kasar Argentina da Portugal sun samu zuwa Gasar Duniya

Kasar Ronaldo ta Portugal ta samu zuwa Gasar Duniya

Kasar Faransa ta isa Gasar da za a buga shekara mai zuwa bayan ta ci wasan ta na karshe a jiyan. Kasashe dai sama da 12 ne dai su ka samu kai wa Gasar cin Kofin Duniya da za a buga a kasar Rasha a shekarar 2018 wanda ciki Najeriya ce ta fara samun tafiya a Nahiyar Afrika.

Kwanaki kun ji cewa manyan ‘Yan wasan Duniya irin su Cristiano Ronaldo na Portugal da Lionel Messi na Argentina su na cikin rudu na kai wa Gasar Duniya na World Cup.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Layin man fetur da ta kuno kai a Abuja ta fara raguwa sosai a halin yanzu

Layin man fetur da ta kuno kai a Abuja ta fara raguwa sosai a halin yanzu

Layin man fetur da ta kuno kai a Abuja ta fara raguwa sosai a halin yanzu
NAIJ.com
Mailfire view pixel