Rundunar Sojin Najeriya ta aika bataliya zuwa Yankin Legas

Rundunar Sojin Najeriya ta aika bataliya zuwa Yankin Legas

- Rundunar Operation Crocodile Smile ta shiga Jihar Legas da Ogun

- A karshen makon jiya aka kaddamar da Rundunar a Yankin Kasar

- Haka kuma Rundunar Sojin na sintiri a Yankin Kudu maso Kudu

Kwanaki mu ka ji cewa Sojojin Najeriya ta zuba Runduna guda a Yankin kudu maso Yammacin kasar nan domin inganta tsaro. Rundunar da ke Yankin dai ta nemi hadin kan Jama'a domin inganta harkar tsaro a Yankin na Kudu maso yamma.

Rundunar Sojin Najeriya ta aika bataliya zuwa Yankin Legas

Rundunar Operation Crocodile Smile ta isa Legas

Rundunar Operation Crocodile Smile sahu na II ta shiga Jihar Legas da Ogun da ke Kudancin Kasar a karshen makon jiya. Ana sa ran Sojojin za su gama sintirin na su ne bayan makonni 3 da aka kaddamar da su.

KU KARANTA: Ko ka san irin horon da ake yi wa Sojoji?

Shugaban Bataliyar Laftana-Kanal Olaolu Daudu a farkon makon nan ya bayyana cewa wannan sintiri zai ba Sojoji damar atisaye da wasa jini sannan kuma su kara kwarewa a harkar shiga fagen daga musamman a Yankunan da ruwa ya ratsa.

Sojojin dai sun bayyana cewa ba za su taba wani dan gari sa ke sha'anin sa ba kamar yadda ta aika Sojoji na musamman na tawagar Operation crocodile smile II zuwa Jihohi 6 na bangaren Neja-Delta domin kawo karshen tsageranci a Kasar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
An fara samun sauki a gidajen man fetur da ke birnin tarayya, Abuja

An fara samun sauki a gidajen man fetur da ke birnin tarayya, Abuja

Layin man fetur da ta kuno kai a Abuja ta fara raguwa sosai a halin yanzu
NAIJ.com
Mailfire view pixel