Mai magana da bakin Jonathan ya tattauna game da sa-in-sar Kachikwu da Baru

Mai magana da bakin Jonathan ya tattauna game da sa-in-sar Kachikwu da Baru

- Reuben Abati yayi magana kan rikicin Ministan mai da Shugaban NNPC

- Abati ya bayyana yadda Kachikwu ya ragewa Baru matsayi a lokacin sa

- Mai magana da bakin Jonathan yace Shugaba Buhari yayi babban kuskure

Mai magana da yawun Shugaba Goodluck Jonathan ya sa baki game da rikicin Shugaban NNPC Maikanti Baru da kuma Ministan mai Ibe Kachikwu a wani rubutu da yayi a wannan makon. A cewar Reuben Abati tun farko Shugaba Buhari yayi kuskure da ya su yin aiki tare da juna.

Mai magana da bakin Jonathan ya tattauna game da sa-in-sar Kachikwu da Baru

Dr. Maikanti Baru da Minista Dr. Ibe Kachikwu

A lokacin Kachikwu yana Shugaban NNPC ya ragewa Baru matsayi duk da yana cikin manyan Ma'aikata a NNPC sai kuma ga shi daga baya Shugaba Buhari ya daga Baru bayan Kachikwu ya zama karamin Ministan mai. A cewar Abati dole a samu matsala a tsakanin su tun daga nan.

KU KARANTA: Hadimin Jonathan yace Shugaba Buhari ne matsalar kasar nan

Sannan kuma dai Ibe Kachikwu karamin Ministan ne wanda ke nufin Maikanti Baru zai rika ganawa ne da babban Minista watau Shugaba Buhari kai tsaye kuma haka aka yi yayin da karamin Ministan ya zama ganawa da Shugaban yana masa wuya.

Abati ya bayyana yadda Ministoci da dama su ka gaza aiki karkashin wasu a don haka su ka dauka daga mukamin su a Kasar a baya. Sai dai a jiya an ga Maikanti Baru da Ibe Kachikwu sun rungume juna a wajen wani taro.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Yadda ganawar Shugaba Buhari da Inyamuran APC ta kasance

Yadda ganawar Shugaba Buhari da Inyamuran APC ta kasance

Abin da Shugaba Buhari ya fadawa ‘Yan APC na Kasar Inyamurai a Villa
NAIJ.com
Mailfire view pixel