Wake ɗaya shi ke bata miya: Asirin wasu Ýansanda 2 da Sojan ruwa 1 masu satar mutane ya tonu

Wake ɗaya shi ke bata miya: Asirin wasu Ýansanda 2 da Sojan ruwa 1 masu satar mutane ya tonu

Rundunar Yansandan jihar Kogi ta bayyana wasu jami’an Yansanda guda 2 da wani Sojan ruwa da aka kama su da aikata laifin satar mutane, tare da yin garkuwa dasu, inji rahoton Daily Trust.

Cikin mutanen da aka kama tare da Yansandan da Sojan, akwai wasu guda 15, wandanda ake zarginsu da aikata laifukan sata, fashi da makami da kuma kashe kashen rayukan jama’a.

KU KARANTA: An sallami yan majalisa guda 2 daga majalisar dokokin jihar Sakkwato

Majiyar NAIJ.com ta ruwaito kwamishinan Yansandan jihar, Ali Janga ya bayyana cewa sun kama miyagun mutanen ne a wurare daban daban na jihar, inda yace Yansandan da aka kama sun hada da Kofur Suleman Isiaka da Ibrahim James sai kuma Kurtun Soja Habila Bature.

Wake ɗaya shi ke bata miya: Asirin wasu Ýansanda 2 da Sojan ruwa 1 masu satar mutane ya tonu

Masu garkuwa

Dansandan da aka kama, Suleman Isiaka yace shi yana bakin aiki ne a garin Bauchi, inda wani abokinsa Shehu Agaba dake kauyen Egume, na karamar hukumar Dekina ya gayyace shi yazo su yi satar mutane.

Isiaka wanda shine ya janyo Habila da Ibrahim cikin aikin yace talauci ne ya kai shi ga aikata wannan mummunan aikin, inda yace a yanzu haka ba shi da komai, biyo bayan wani gobara dayua lakume gidansa.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.naij.com

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Dandalin Kannywood: Atiku ne kadai ke da mabudin gyaran Najeriya - Fati Muhammad

Dandalin Kannywood: Atiku ne kadai ke da mabudin gyaran Najeriya - Fati Muhammad

Dandalin Kannywood: Atiku ne kadai ke da mabudin gyaran Najeriya - Fati Muhammad
NAIJ.com
Mailfire view pixel