Kudaden da aka karbo wajen masu satar dukiyar gwamnati na shiga cikin kasafin kudi na 2017- Gwamnatin Tarayya

Kudaden da aka karbo wajen masu satar dukiyar gwamnati na shiga cikin kasafin kudi na 2017- Gwamnatin Tarayya

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayar da sanarwar cewa, gwamnatinsa ta na amfani da wani kaso na kudaden da aka karbo daga hannun masu satar dukiyar gwamnati wajen marawa kasafin kudi na 2017.

A ranar Talata 10 ga watan Oktoba, Shugaban lissafin kudi na kasa baki daya Alhaji Idris Ahmed, wanda ya wakilci shugaban kasar ya bayyana hakan ne a wurin wani taron masana lissafin kudi da aka gudanar a birnin Tarayya.

Shugaban ya bayyana cewa, gwamnati ta na amfani da wani kaso na kudin da ta karbo daga hannun wadanda suka sace dukiyar gwamnati domin marawa kasafin kudi na 2017.

Mu na marawa kasafin kudi na 2017 da kudaden da aka karbo wajen masu satar dukiyar gwamnati - Gwamnatin Tarayya

Mu na marawa kasafin kudi na 2017 da kudaden da aka karbo wajen masu satar dukiyar gwamnati - Gwamnatin Tarayya

A kalaman shugaban kasar, "gwamnatinsa ta yi hobbasa kwarai da aniyya wajen habaka tattalin arzikin kasa".

KARANTA KUMA: Ministan man Fetur ya yi wata ganawa da shugaban NNPC

"Idan aka duba karfin samar da wutar lantarki ya karuwar da bai taba yi ba a tarihi zuwa ma'aunin wutar lantarki 7001 na megawatts, wanda muke sa ran ya zai karu zuwa ma'auni 10, 000 na megawatts a shekarar 2020".

Idris ya kara da cewa, samar da asusun gwamnati guda a watan Satumba na shekarar 2015 domin ajiyar dukiyar gwamnati ya taimaka kwarai wajen fayyace komai a fili musamman yadda gwamnatin take gudanar da al'amurran dukiyar al'umma.

Domin shawara ko bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA

An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA

An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA
NAIJ.com
Mailfire view pixel