Dalilin da yasa naki yadda in fita kasar waje neman lafiya - Aisha Buhari

Dalilin da yasa naki yadda in fita kasar waje neman lafiya - Aisha Buhari

Uwar gidan shugaba Muhammadu Buhari Aisha Buhari ta bayyana musabbabin dalilin da ya sa taki amincewa ta fita kasashen waje domin neman lafiyar ta a kwanan baya lokacin da bukatar hakan ta taso.

Uwar gidan ta shugaba Buhari ta bayyana dalilin nata be a yayin da take jawabi a wajen wani taron habaka lafiyar yara da kuma mata a dakin taro na fadar shugaban kasar a ranar Litinin din da ta gabata.

Dalilin da yasa naki yadda in fita kasar waje neman lafiya - Aisha Buhari

Dalilin da yasa naki yadda in fita kasar waje neman lafiya - Aisha Buhari

KU KARANTA: Ahmad Musa ya bude gidan mai a Kano

NAIJ.com ta samu dai cewa Aisha Buhari tace: "Kwanakin da suka wuce nayi wata 'yar rashin lafiya amma sai aka bani shawarar in fita zuwa Landan kawai a duba ni amma sai naki nace a asibitin gwamnati zan je don kuwa akwai kudaden da ake ware masu."

Ta ci gaba da cewa: "Da naje sai suka fada mani cewa wai na'urar daukar hoton bata aiki. Atakaice dai sai da na je asibitin da wasu yan kasar waje suka bude sannan na samu cikakkiyar kulawa."

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Layin man fetur da ta kuno kai a Abuja ta fara raguwa sosai a halin yanzu

Layin man fetur da ta kuno kai a Abuja ta fara raguwa sosai a halin yanzu

Layin man fetur da ta kuno kai a Abuja ta fara raguwa sosai a halin yanzu
NAIJ.com
Mailfire view pixel