Hatsarin jirgin ruwa ya yi sanadin rai 1 tare da jigata 19 a jihar Legas

Hatsarin jirgin ruwa ya yi sanadin rai 1 tare da jigata 19 a jihar Legas

Mutum guda ya riga mu gidan gaskiya tare da jigatar mutane 19 yayin da wani jirgin ruwa dauke da fasinjoji 20 ya dilmiye a ranar Talatar yau a jihar Legas.

Rahotanni sun bayyana cewa, wannan jirgin ya kife ne a tekun Mainland Bridge na uku dake jihar ta Legas.

Shugaban hukumar kula da harkokin tekun Legas (Lagos State Waterways Authority) Damilola Emmanuel, ya tabbatar da mutuwar wannan fasinja guda yayin da sauran fasinjojin da aka ceto an kuma garzaya da su asibiti domin duba lafiyarsu.

Hatsarin jirgin ruwa ya yi sanadin rai 1 tare da jigata 19 a jihar Legas

Hatsarin jirgin ruwa ya yi sanadin rai 1 tare da jigata 19 a jihar Legas

Damilola ya bayyana cewa, hukumar za ta dauki matakai na kwarai domin magance faruwar ire-iren wannan ibtila'i a karo na gaba, tare da hadin gwiwar gwamnatin jihar da zata tabbatar da cewar ma'aikatan hukumar sun kinyaye dukkan wata doka da za a tanadar wajen magance wannan matsala.

KARANTA KUMA: Zaben 2019: Tsohon gwamnan jihar Abia ya yi wata ganawar sirrance da IBB

NAIJ.com ta fahimci cewa, a ranar Larabar da ta gabata ne gwamnatin jihar Legas ta zartar da doka domin hana dukkan wasu matukan jirgin ruwa amfani da tashohin jiragen ruwan ba bisa ka'ida ba, domin a cewar gwamnatin ire-iren wannan karyar dokar ya na kara hasala faruwar ibtila'i.

Domin shawara ko bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Canji: Hotunan ƙarin sabbin taragon jirgin kasa na Abuja-Kaduna sun iso Najeriya

Canji: Hotunan ƙarin sabbin taragon jirgin kasa na Abuja-Kaduna sun iso Najeriya

Canji: Hotunan ƙarin sabbin taragon jirgin kasa na Abuja-Kaduna sun iso Najeriya
NAIJ.com
Mailfire view pixel