Yanzu Yanzu: Ministan man Fetur ya yi wata ganawa da shugaban NNPC

Yanzu Yanzu: Ministan man Fetur ya yi wata ganawa da shugaban NNPC

NAIJ.com ta samu rahoton cewa bayan a jiye banbance-banbancensu a gefe, Karamin ministan man fetur Mista Ibe Kachikwu da kuma Mista Maikanti Baru, wanda shine shugaban kamfanin man fetur na Najeriya (NNPC), sun shiga tattaunawa domin karkata akalar sashen harkokin man fetur na kasa zuwa ga wani munzali na ci gaba.

Wannan shugabannin biyun sun hadu a wani taron tattaunawa akan habaka tattalin arzikin Najeriya da akan gudanar a birnin tarayya Abuja, inda haduwarsu ke da wuya suka yi musayar musafaha da juna tare da nuna farin ciki.

Rahotanni sun bayyana cewa, ministan ya bar dakin taon ne tun kafin a tashi, sai kuma daga bisani ya dawo kuma su ka yi wata tattaunawa ta tsawon dakikai kadan tare da shugaban kamfanin na man fetur sannan kowa ya kama gabansa.

Yanzu Yanzu: Ministan man Fetur ya shiga ganawa da shugaban NNPC

Yanzu Yanzu: Ministan man Fetur ya shiga ganawa da shugaban NNPC

KARANTA KUMA: Gwamnatin Tarayya za ta sa kafar wando daya da masu magungunan jabu

A jawaban da minista kachikwu, ya bayyana cewa sashen kula da harkar man fetur na kasa yana hobbasa wajen habakarsa a kullum, inda kuma ya ce gwamnatin tarayya ta na iya ka cin bakin kokarin wajen kawo tsare-tsare da zasu 'yan kasuwa wajen sayen man fetur din.

Domin shawara ko bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59

Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59

Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59
NAIJ.com
Mailfire view pixel