Kotu ta umarci bankuna da su bude asusun ajiyar Peace Corps

Kotu ta umarci bankuna da su bude asusun ajiyar Peace Corps

Wata babbar kotu dake zamanta a Abuja karkashin mai shari'a John Dantsoho ta bayar da umarnin bude asusun ajiya 24 mallakin Peace Corps da aka rufe biyo bayan wata takardar kotu da hukumar'yan sanda ta gabatar ga bankunan a ranar 23 ga watan yuni da ya gabata.

A ranar 5 ga watan yuli ne, John Ojogu, ya shigar da kara gaban kotun a madadin Peace Corps, yana neman kotu data hana bankuna aiki da waccan takarda da hukumar'yan sanda ta gabatar tare da umartar bankunan Diamond da Stanbic IBTC da su bude ma su asusun ajiyar su.

Kotu ta umarci bankuna da su bude asusun ajiyar Peace Corps

Kotu ta umarci bankuna da su bude asusun ajiyar Peace Corps

Da yake yanke hukunci, Dantsoho ya ce kotu ta dogara ne da gazawar lauyan hukumar 'yan sanda na kasa gabatar da cikakkiyar shaidar cewar ministan shari'a na kasa ya saka hannu a takardar umarnin kotu na rufe asusun ajiyar Peace Corps, a saboda haka kotu ta amince da hujjar lauyan Peace Corps cewar rufe asusun ajiyar na wucin gadi ne, kuma lokacin ta ya shude.

DUBA WANNAN: Ku bani shawara: Baturiya ta yi alkawarin bani miliyan 145 idan har na amince zan auri 'yar ta

Dantsoho ya ce "A saboda haka idan hukumar 'yan sanda nada wata bukata nan gaba tana iya gabatar da ita ta hanyar rubutaccen korafi amma ba ta hanyar neman hukuncin gaggawa mai takaitaccen lokaci ba".

Mai shari'a Dantsoho ya rufe da cewa, "A saboda haka wannan kotu ta karbi korafin hukumar Peace Corps, ta jingine wancan hukunci na farko da ya bayar da damar rufe asusun ajiyar Peace Corps".

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Source: Hausa.naija.ng

Related news
An fara samun sauki a gidajen man fetur da ke birnin tarayya, Abuja

An fara samun sauki a gidajen man fetur da ke birnin tarayya, Abuja

Layin man fetur da ta kuno kai a Abuja ta fara raguwa sosai a halin yanzu
NAIJ.com
Mailfire view pixel