An sallami yan majalisa guda 2 daga majalisar dokokin jihar Sakkwato

An sallami yan majalisa guda 2 daga majalisar dokokin jihar Sakkwato

- Majalisar dokokin jihar Sakkawato ta fatattaki wasu yayanta guda biyu

- Yan majalisar sun hada da Sani Yakubu da Malami Galandanci

Majalisar dokokin jihar Sakkawato ta fatattaki wasu yayanta guda biyu kan zarginsu da rashin da’a da tayi, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Yan majalisan da aka sallama sun hada da Sani Yakubu dake wakiltar al’ummar Gudu da aka sallame shin a tsawon kwanaki 40, da kuma Malami Galandanci dake wakiltar Sakkwato ta kudu I da aka dakatar da shin a tsawon kwanaki 30.

KU KARANTA: Soja marmari daga nesa: Kalli horon da ake baiwa Sojojin Najeriya

Majalisar ta yanke shawarar sallamar su ne bayan rahoton wani kwamitin mutane 11 da aka kafa, wanda ya binciki rawar da suka taka wajen tunbuke mataimakin shugaban masu rinjaye na majalisar.

An sallami yan majalisa guda 2 daga majalisar dokokin jihar Sakkwato

Yan majalisar dokokin jihar Sakkwato

Yan majalisun su biyu sun yi ruwa sun yi tsaki wajen ganin ba’a tunbuke mataimakin shugaban masu rinjaye na majalisar ba, inda suka ce wata hanya ce kawai don Kaakakin majalisar ya kare kansa daga wata ta’asa daya tafka.

Haka zalika majalisar ta bukaci yayan nata guda da su nemi gafarar majalisar tare da bata hakuri. Sai dai da majiyar NAIJ.com ta tuntubi Galadanci, sia yace “Ba zan ce komai dangane da wannan batu ba a yanzu.”

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.naij.com

Gidan Fela: Kalla a NAIJ.com TV

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Dandalin Kannywood: Atiku ne kadai ke da mabudin gyaran Najeriya - Fati Muhammad

Dandalin Kannywood: Atiku ne kadai ke da mabudin gyaran Najeriya - Fati Muhammad

Dandalin Kannywood: Atiku ne kadai ke da mabudin gyaran Najeriya - Fati Muhammad
NAIJ.com
Mailfire view pixel