Kotu ta zartar da wani tsatsauran hukunci akan gwamnatin tarayya

Kotu ta zartar da wani tsatsauran hukunci akan gwamnatin tarayya

Kotun hadin kan kasashen Afirka ta Yamma (ECOWAS), ta baiwa gwamnatin Najeriya umarnin biyan diyya ga wani babban sojin sama Danladi Angulu Kwasu, sanadiyar mutuwar dan sa Elshadai Kwasu.

Elshadai mai shekaru 19 da haihuwa a duniya, dalibin makarantar shiga aikin soji ce ta (Nigerian Defence Academy, NDA), wanda ya ce ga garinku nan a ranar 30 ga watan Afrilun shekarar 2015 inda ya dilmiye cikin ruwa yayin koyon iyo a makarantar.

Shafin Premium Times ya ruwaito cewa, kotun ta baiwa gwamnatin Najeriya umarnin biyan Dalar Amurka 75, 000 ga ahalin wannan mamaci sakamakon rashin kulawa da hakkin rayuwa ta wannan dalibi. Ta kuma umarci gwamnatin akan ta tsananta bincike domin gano ainihin sanadaiyar mutuwarsa tare da daukan matakai akan wadanda suke da hannu a wajen rashin kulawar.

NAIJ.com ta fahimci cewa mahaifin wannan dalibin Danladi, shine ya shigar da karar ga kotun domin shi a ganinsa an ketawa marigayin dan sa hakkinsa na yin rayuwa.

Kotu ta zartar da wani tsatsauran hukunci akan gwamnatin tarayya

Kotu ta zartar da wani tsatsauran hukunci akan gwamnatin tarayya

Sai dai lauya mai kare gwamnatin ta Najeriya ya bayyana cewa, akwai yarjejeniya da aka kafa tsakanin iyayen wannan dalibi da hukumar makarantar ta NDA wajen yiwar afkuwar hatsarurruka makamantan wannan, wanda daman ya na cikin tsarin shiga makarantar.

KARANTA KUMA: Labarai cikin Hotuna: Matashi yayi fasahar kera jirgin sama a jihar Yobe

Ita kuwa kotu tayi watsi da wannan batu na lauyan, inda ta ce duk da cewa akwai yarjejeniya tsakanin iyayen dalibai da hukumar makaranta, ya kuma kamata ace akwai tsare-tsare da aka kafa wajen lura daga bangaren gwamnatin.

Akwai mutane uku da Nwoke Chijioke ya jagoranta a matsayin masu wakiltar mai shigar da kara, wanda suka tabbatar da cewa an tursasa wannan marigayin dalibin wajen shiga cikin bayan da akwai masaniyar bai iya iya iyo a cikin ruwan ba.

Domin shawara ko bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
An fara samun sauki a gidajen man fetur da ke birnin tarayya, Abuja

An fara samun sauki a gidajen man fetur da ke birnin tarayya, Abuja

Layin man fetur da ta kuno kai a Abuja ta fara raguwa sosai a halin yanzu
NAIJ.com
Mailfire view pixel