Wasu matasa a Kano sun jefe wani mutumi mai shekaru 70 har lahira

Wasu matasa a Kano sun jefe wani mutumi mai shekaru 70 har lahira

Wasu matasan Kanawa sun kashe wani mutumi mai suna Usman Danbuba, bayan da suka sace shi, suka yi garkuwa da shi a jihar Kano, inji jaridar Daily Trust.

Matasan da aka ruwaito sunayensu, sun hada da Wada Mohammed, Ya’u Muhammad, Musa Inusa, Sale Buba da kuma Sule Garba sun gurfana gaban kotun majistri dake jihar Kano a ranar Talata 10 ga watan Oktoba.

KU KARANTA: Soja marmari daga nesa: Kalli horon da ake baiwa Sojojin Najeriya

Ana tuhumar matasan ne da laifin hadin baki wajen aikata mummunan laifi, yin garkuwa da mutum, fashi da makami, kisan kai da kuma mallakan makami ba akan ka’aida ba.

Wasu matasa a Kano sun jefe wani mutumi mai shekaru 70 har lahira

Masu garkuwa da mutane

Majiyar NAIJ.com ta ruwaito a ranar 18 ga watan Mayu ne aka sace Dattijo Usman Danbuba mai shekaru 70 a karamar hukumar Doguwa na jihar Kano, inda suka barayin suka diran ma Dattijon da bindiga da kuma adduna a gidansa, inda suka kwace masa N85,000 da babur.

“Bayan sun sace shi, sai suka kai shi mabuyarsu dake karkasgin dutsen Shetu dajin Falgore, jihar Kano, inda suka bukaci a basu naira miliyan 5. Amma da suka fahimci iyalansa basu da kudin, sai suka halaka shi ta hanyar jifa da duwatsu.” Inji Dansanda mai shigar da kara.

Dansandan ya kara da cewa akwai wani Iliyasu Moshede da ake nema yanzu haka, yana daya daga cikin yan fashi, sai dai gaba daya mutanen da aka kama sun musanta tuhume tuhumen da ake yi musu.

Bayan saurarin dukkan bangarorin, Alkalin kotun Aminu Fagge ya dage sauraron karar zuwa 23 ga watan Oktoba.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.naij.com

Yadda aka kama shugaban masu garkuwa da mutane, Evans,

Source: Hausa.naija.ng

Related news
An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA

An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA

An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA
NAIJ.com
Mailfire view pixel