'Duk zancen IPOB kokarin Igbo ne na kwace wa Buhari mulki a 2019' Junaidu Muhammed

'Duk zancen IPOB kokarin Igbo ne na kwace wa Buhari mulki a 2019' Junaidu Muhammed

Kungiyar IPOB dai sune ke son lallai sai an kafa kasar Bayafara a yankin gabashin Najeriya, karkashin shugabancin NNamdi Kanu wanda ya tsere kasar Ingila a makonnin baya. Junaidu Muhammed ya ce ai duk ba don Biafra ake yi karadin ba, wai don Ibo su kwaci mulki a 2019 ne.

'Duk zancen IPOB kokarin Igbo ne na kwace wa Buhari mulki a 2019' Junaidu Muhammed

'Duk zancen IPOB kokarin Igbo ne na kwace wa Buhari mulki a 2019' Junaidu Muhammed

Junaidu Muhammed, tsohon dan majalisa ne ta kasa tun a jamhuriyya ta biyu, kuma gogaggen dan siyasa na arewa. A tsokacinsa, ya ce ai ba Biafra kabilar Ibo ke wa karadi ba, wai ai so suke lallai sai an basu takara kuma an zabe su mulkin shugabancin Najeriya a 2019.

A fadinsa, wai babu yadda za'ayi kabilar Ibo ya sake mulkar kasar nan, tunda su suka kawo wa Najeriya cikas da yawa a baya. Ya kuma ce babu ja da baya, mulki a arewa zai zauna har bayan 2019.

DUBA WANNAN: Baru ya zargi Kachiku da tunzura 'yan Najeriya

Ana ganin dai Atiku yake ma aiki, domin yana yawan caccakar shugaba Buhari, kuma ma ya nuna karara kishin arewa yake yi.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Source: Hausa.naija.ng

Related news
An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA

An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA

An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA
NAIJ.com
Mailfire view pixel