2019: Kai ne babban matsalar Najeriya; Omokri ya caccaki Buhari

2019: Kai ne babban matsalar Najeriya; Omokri ya caccaki Buhari

- Reno Omokri ya caccaki shugaba Muhammadu Buhari a matsayin babban matsalar Najeriya

- Omokri ya gudanar da zabe a yanar gizo a kan babbar kalubalen da ke fuskantar Najeriya kafin 2019

- Omokri ya ce, 'yan Najeriya sun zabi Buhari kashi 43% a sakamakon zaben

Reno Omokri, tsohon mai ba da shawara ga tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan, ya bayyana cewa shugaba Muhammadu Buhari ne babban matsala da ke fuskantar Najeriya.

NAIJ.com ta tattaro cewa, Omokri ya bayyana hakan, bayan sakamakon wani zaben da ya gudanar a yanar gizo a kan babbar kalubalen da ke fuskantar Najeriya kafin 2019.

Faston wanda ke zaune a kasar Amurka ya yi wannan sanarwar a cikin jerin rubutu a shafinsa ta Twitter.

2019: Kai ne babban matsalar Najeriya; Omokri ya caccaki Buhari

Reno Omokri

Kamar yadda tsohon ma shawarcin ya yi tambaya a zaben,ya ce, "Yadda 2019 ke gabatowa, menene kuke tsammanin babbar kalubalen da ke fuskantar Najeriya?"

KU KARANTA: Yanzu Yanzu: Buhari ya nemi yardan majalisar dokoki domin nemo rancen naira triliyan 2.3

Omokri ya ba da zaɓi hudu wanda ya haɗa da: Rashin aikin yin, cin hanci da rashawa, ta'addanci da kuma Buhari.

Da yake bayyana sakamakon zaben, Omokri ya ce, 'yan Najeriya sun zabi Buhari kashi 43%.

Bayan wannan sakamakon, Omokri ya ce, "Ba mu da shugaba a PMB. Muna da matsala a gare shi! ", kamar yadda ya rubuta.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
A faɗa a cika: Minista Amaechi ya cika alƙawarin shigo da sabbin taragon jirgin kasa na zamani

A faɗa a cika: Minista Amaechi ya cika alƙawarin shigo da sabbin taragon jirgin kasa na zamani

Canji: Hotunan ƙarin sabbin taragon jirgin kasa na Abuja-Kaduna sun iso Najeriya
NAIJ.com
Mailfire view pixel