Wata kungiya ta musulmi zata tono gawar mutumin da kwarankwatsa ta fadowa

Wata kungiya ta musulmi zata tono gawar mutumin da kwarankwatsa ta fadowa

- Ma'aikaci da aradu ta adowa ya rasa ransa

- Sai da aka yi cece-kuce kan binne gawar tasa

- Wai an binne shi ne a makabartar kirista saboda yadda ya mutu

A Ilorin din jihar Kwara ne aka sami takaddama tsakanin musulmai da kirista kan gawar wani dan tahaliki da tsawa ta fadowa, inda ya rasa ransa sakamakon hakan.

Wata kungiya ta musulmi zata tono gawar mutumin da kwarankwatsa ta fadowa

Wata kungiya ta musulmi zata tono gawar mutumin da kwarankwatsa ta fadowa

Malam Salami Adekunle dai ya rasa ransa ne bayan da tsawa ta ffado masa ana ruwa, a garinsu na Oro, da ke Irepodun LG a jihar ta Kwara, kafin rasuwarsa kuma, yana aiki ne a kwalejin koyarwa ta jihar.

An dai binne gawar malamin ne a makabartar kirista bayan da masu chamfi ke ganin kamar mutuwar tashi na da alaka da wani hukunci daga sama, inda aka rufe shi babu sutura babu kuma wankan gawa.

Sai dai Dr. Abubakar Aliagan, Lakchara a jami'ar ta Ilorin, kuma mai kula da harkokin makabartu na musulmi a yankin, yace zasu tono gawar malamin, su kuma yi masa sutura kamar yadda addinin musulunci ya tanada.

DUBA WANNAN: Rikicin baru na NNPC da kachiku ministan mai

Ita dai tsawa da aradu, haji ne na lantarki da ke yawo cikin ruwa, yakan kuma sauka kan ko menene domin kokarinsa, ya koma cikin kasa, idan aka yi ashin sa'a ya fadowa gini ko bishiya ko mutum, shocking ko gobara na iya biyo baya, da ma asarar rayuka.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https ://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Dandalin Kannywood: Atiku ne kadai ke da mabudin gyaran Najeriya - Fati Muhammad

Dandalin Kannywood: Atiku ne kadai ke da mabudin gyaran Najeriya - Fati Muhammad

Dandalin Kannywood: Atiku ne kadai ke da mabudin gyaran Najeriya - Fati Muhammad
NAIJ.com
Mailfire view pixel