Cutar ‘Monkey Pox’ ya yadu zuwa jihohi 7 na kasar nan

Cutar ‘Monkey Pox’ ya yadu zuwa jihohi 7 na kasar nan

- Cutar Monkeypox na cigaba da yaduwa cikin sauri a Najeriya

- Hukumar NCDC ta rahoto cewa me yiwuwa cutar ya yadu a akalla jihohi 7

- Ana cigaba da gudanar da bincike akan cutar

A ranar Litinin, 9 ga watan Oktoba,Shugaban hukumar dake hana yaduwar cututtuka na kasa baki daya, Chikwe Ihekweazu ya sanar da cewa akalla mutane 31 ne suka kamu da cutar ‘Monkey Pox’ daga jihohi 7 a fadin kasar.

Jaridar Cable ta ruwaito cewa anyi zargin bullar cutar a jihohi 6 bayan inda aka fara gano cutar a Bayelsa a ranar 22 ga watan Satumba.

Jihohin da ya lissafa sun hada da:

1. Bayelsa

2. Rivers

3. Ekiti

4. Akwa Ibom

5. Lagos

6. Ogun

7. Cross River

A cewar Ihekweazu babu mamaki ba kowanen su ne ke dauke da wannan cuta ta ‘Monkey Pox’ sai dai an ajiye su ne zuwa lokacin da za’a kammala gudanar da bincike.

Yace: “Cutar ‘Monkey Pox’ ya bazu zuwa jihohi 7 sannan bayan haka zamu san irin matakin da ya kamata mu dauka.

”Duk da hakan babu wanda ya mutu cikin wadanda ke dauke da cutar sannan wasu cikinsu sun fara samun sauki daga cutar saboda samun kula a asibitocin da suke kwance.”

KU KARANTA KUMA: Victor Moses da Shehu Abdullahi sun shiga cikin jarumai goma sha daya na kungiyar CAF

Daga karshe Ihekweazu ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su kwantar da hankalinsu su kuma hanzarta kai duk wanda suke ganin ya kamu da cutar zuwa asibiti mafi kusa da su sannan kuma su guji shan magani batare da izinin wani ma’aikacin kiwon lafiya ba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Illar cin hanci: Sojan Najeriya ya bindige wani Mahauci a kan ya hana shi N500 na goro (Hoto)

Illar cin hanci: Sojan Najeriya ya bindige wani Mahauci a kan ya hana shi N500 na goro (Hoto)

Illar cin hanci: Sojan Najeriya ya bindige wani Mahauci a kan ya hana shi N500 na goro (Hoto)
NAIJ.com
Mailfire view pixel