Yadda gudanarwar sojin kasa ta dakile ta'addanci a yankin Kudu Maso Gabas - Bincike

Yadda gudanarwar sojin kasa ta dakile ta'addanci a yankin Kudu Maso Gabas - Bincike

A wani sabon rahoto da wata kungiyar kare hakkin dan Adam ta fitar ya bayyana cewa, gudanarwar nan mai taken Rawar Damatsiri ta biyu (Python Dance II) da dakarun sojin kasa ke aiwatar a yankunan Kudu Maso Gabashin kasar ta yi tasirin dakile tayar da zaune a yankin.

Binciken ya bayyana cewa, gudanarwar da sojin kasan ke aiwatarwa ta kwantar da tarzomar laifukan garkuwa da mutane, kashe-kashe na kungiyar asiri, fashi da makami da sauran nau'ukan ta'addanci a fadin yankin.

A wannan sabon rahoton da kungiyar kare hakkin dan Adam ta Independent Human Rights/ Crime Monitoring Group in Nigeria, IHRCMG ta bayyana cewa, dakarun sojin Najeriya sun yi nasarori da dama wajen kawo kwanciyar hankulla ga al'ummar kasar nan.

Yadda gudanarwar sojin kasa ta dakile ta'addanci a yankin Kudu Maso Gabas - Bincike

Yadda gudanarwar sojin kasa ta dakile ta'addanci a yankin Kudu Maso Gabas - Bincike

A yayin gabatar da wannan rahoton a ranar Talata 10 ga watan Oktoba, shugaban kungiyar ta IHRCMG Zineke Werigbelegha ya bayyana cewa, wannan gudanarwar da dakarun sojin ke aiwatarwa ba karamin alfanu ne ga al'ummar kasar nan ba. Shugaban ya bayyana cewa wannan gudanarwar ta taimaka wajen dakile tayar da zaune tsayen da hukumar 'yan sanda ta sha fama da ita.

KARANTA KUMA: Labarai cikin Hotuna: Matashi yayi fasahar kera jirgin sama a jihar Yobe

Werigbelegha ya ce, kungiyar ta tabbatar da wannan rahoton ne bayan da ma'aikatan ta suka shiga yawan zagaye a jihohi biyar na yankin Kudu Maso Gabas wadanda suka hadar da; Imo, Enugu, Ebonyi, Anambra da kuma Abia. Sa'annan sun kara nutsawa cikin wasu yankunan jihohin Rivers, Akwa-Ibom da Cross River.

Kungiyar ta IHRCMG ta kara da cewa, ya kamata wannan dakarun soji su rinka makamanciyar wannan gudanarwar lokaci bayan lokaci domin hakan zai taimaka matuka wajen tarwatsa dukkan wata kungiyar ta'adda.

Domin shawara ko bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59

Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59

Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59
NAIJ.com
Mailfire view pixel