Kudin asusun kasar wajen Najeriya yana cigaba da habaka

Kudin asusun kasar wajen Najeriya yana cigaba da habaka

- Kudin kasar wajen Najeriya na cigaba da karuwa

- A wannan watan ma Dalolin Najeriya sun karu

- Duk da tsarin CBN abubuwa na mikewa a kasar

A fannin tattalin arziki dai mun samu labari cewa kudin asusun kasar wajen Najeriya yana cigaba da habaka a wannan wata.

Kudin asusun kasar wajen Najeriya yana cigaba da habaka

Tattalin Najeriya yana habaka a sannu

Bisa dukkan alamu duk da tsarin babban bankin kasar na CBN na sakin Dalolin da aka samu kasuwar canji, abubuwa na mikewa a kasar a wannan wata da aka shiga. Yanzu haka kudin kasar wajen da Najeriya ta mallaka ya kai Dala Biliyan 32.75.

KU KARANTA: Hanyoyi 25 da Gwamnati Shugaba Buhari za ta gyara

An dai samu karuwar kudin daga farkon shekarar nan zuwa yanzu kwarai da gaske. A karshen watan jiya dai Najeriya ta mallaki Dala Biliyan 32.74 a asusun kasar waje. Gangar man fetur dai yana tsakanin Dala $46 zuwa $52 mafi yawan lokaci.

Haka kuma dai Dalar Amurka tana kan kusan N364 a kasuwar canji a kasar. Kwanaki dai Tsohon Shugaban kasa Olusegun Obasanjo yayi magana game da tsarin tattalin Shugaban kasa Buhari inda yace da sake.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
INEC ta kori wasu jami'anta 2 akan yi wa gwamna Bello rajista so biyu

INEC ta kori wasu jami'anta 2 akan yi wa gwamna Bello rajista so biyu

INEC ta kori wasu jami'anta 2 akan yi wa gwamna Bello rajista so biyu
NAIJ.com
Mailfire view pixel