2019: Donald Duke ya kalubalanci shirin mulkin juya juya a Najeriya

2019: Donald Duke ya kalubalanci shirin mulkin juya juya a Najeriya

- Tsohon gwamna na jihar Cross River ya kalubalanci shirin mulkin juya juya

- Duke ya ce bai taba sanya kainsa cikin shirin mulkin karba karba ba

- Tsohon gwamnan ya ce ya kamata a yi watsi da shirin juya juya

Tsohon gwamna na jihar Cross River, Donald Duke, yace ba ya goyon bayan mulkin juya juya na shugaban kasa.

Duke, yayin da yake jawabi a wani shiri wanda aka sani da Hard Copy wanda Maope Ogun ya shirya a gidan telebijin na Channels, ya ce, "Ban taba sanya kaina cikin shirin mulkin karba karba ba, lokacin da na nema takarar gwamna duk masu sha’awar tsaya takara sun fito neman kuriya a Cross River".

Ya ci gaba da cewa, "Baya ga tsarin mulki, ina da hakin tsaya takara, ba za ku iya kwace ‘yanci na saboda wannan shirin ba, mulkin karba karba ta saba wa tsarin mulki”.

2019: Donald Duke ya kalubalanci shirin mulkin juya juya a Najeriya

Tsohon gwamna na jihar Cross River, Donald Duke

"Kamar yadda na ce an haife ni a Najeriya, ba a haife ni yankin kudu maso gabas ko yamma ba, an haife ni bayan samun ‘yanci. Don haka ni cikkaken dan Najeriya ne", inji shi.

KU KARANTA: Zaben 2019: A shirye muke mu sadaukar ran mu domin PDP tayi nasara - Gwamna Wike

Daga bisani, tsohon gwamnan ya ce Najeriya na da matsaloli da dama, kuma ya kamata a yi watsi da wannan shirin kuma.

Ana iya tunawa da cewa manyan jam'iyyar APC da na adawa ta PDP sun yi Allah wadai da gwamna Ayo Fayose na Ekiti don ya bayyana manufarsa na tsaya takara shugaban kasa a shekara ta 2019 wanda ta saba wa shirin karba karba na manyan jam'iyyun biyu a kasar.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Yadda ganawar Shugaba Buhari da Inyamuran APC ta kasance

Yadda ganawar Shugaba Buhari da Inyamuran APC ta kasance

Abin da Shugaba Buhari ya fadawa ‘Yan APC na Kasar Inyamurai a Villa
NAIJ.com
Mailfire view pixel