Gwamnatin Tarayya za ta sa kafar wando daya da masu magungunan jabu

Gwamnatin Tarayya za ta sa kafar wando daya da masu magungunan jabu

- Gwamnati za ta rufe wuraren da aka saida magungunan banza a Kasar

- Ministan lafiya na kasar nan Farfesa Isaac Adewole ya bayyana wannan

- Ba dai yau Gwamnati ta saba gargadin masu saida maganin jabu ba

A makon nan ne mu ka ji cewa za a takawa masu saida magungunan da ba su da kyau a cikin Najeriya zuwa karshen shekarar badi.

Labari ya zo mana cewa Gwamnatin Tarayya za ta kirkiro wasu cibiyoyin da za su rika kula da irin magungunan da ake saidawa cikin kasar nan. Wannan zai bada damar a rika sayen magunguna daga kamfani kai tsaye a Kasar.

KU KARANTA: Amurka na shirin kashe Shugaban Koriya ta Arewa

Ministan lafiya Farfesa Isaac Adewole ya bayyana wannan a wajen wani taron karawa juna sani da Hukumar NAFDAC da WHO ta Duniya ta shirya. A halin yanzu ana saida magunguna ne kurum a kasuwa ba tare da kiyaye abin da ake saidawa ba.

Adewole yace zuwa karshen shekara mai zuwa za a rufe duk wuraren duk inda ‘yan bumburutu ke saida magungunan banza. Ba dai yau Gwamnatin Tarayya ta saba gargadin masu saida maganin jabu ba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Layin man fetur da ta kuno kai a Abuja ta fara raguwa sosai a halin yanzu

Layin man fetur da ta kuno kai a Abuja ta fara raguwa sosai a halin yanzu

Layin man fetur da ta kuno kai a Abuja ta fara raguwa sosai a halin yanzu
NAIJ.com
Mailfire view pixel