Yadda Shugaba Buhari yayi da Gwamna Geidem a Fadar Shugaban kasa

Yadda Shugaba Buhari yayi da Gwamna Geidem a Fadar Shugaban kasa

- Shugaban kasa Buhari ya gana da Gwamnan Jihar Yobe

- Gwamnan ya gana da Shugaban ne a Fadar sa ta Villa jiya

- Shugaba Buhari ya kuma gana da wasu Gwamnonin a ranar

A jiya Litinin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya gana da wasu Gwamnonin kasar nan a fadar Shugaban kasa na Aso Villa.

Yadda Shugaba Buhari yayi da Gwamna Geidem a Fadar Shugaban kasa

Shugaba Buhari ya gana da Gwamnan Jihar Yobe

Daga cikin Gwamnonin da Shugaban ya gana da su akwai Gwamnan Jihar Yobe Ibrahim Geidem. Gwamnan ya nemi Gwamnatin Tarayya ta maido masa da kudin da ya kashe wajen shawo kan sha’anin tsaro saboda rikicin Boko Haram har Naira Biliyan 13 a Jihar.

KU KARANTA: Bincike ya nuna cewa akasarin ‘Yan ta’adda ba Musulmai bane

Gwamnan dai ya kuma yi amfani da wannan damar wajen gaida Shugaban kasar don kuwa ba su samu ganawa ba tun bayan da ya dawo daga jinya. Gwamnan ya bayyana cewa fiye da watanni 2 kenan ba a ji duriyar ‘Yan Boko Haram ba a Jihar Yobe.

Ibrahim Geidem yake cewa a lokacin Gwamnatin Jonathan Jihar ta kashe makudan kudi wajen ayyukan da ya kamata ace Gwamnatin Tarayya tayi don haka yake nema Shugaba Buhari ya maida masu kadan daga abin da su ka kashe domin su gina asibitoci da sauran su.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Ta tabbata' Kasar Iran ke taimakawa 'yan tawayen Kasar Yemen

Ta tabbata' Kasar Iran ke taimakawa 'yan tawayen Kasar Yemen

Ta tabbata' Kasar Iran ke taimakawa 'yan tawayen Kasar Yemen
NAIJ.com
Mailfire view pixel