Jerin hanyoyi 25 da Buhari zai yi, kudin su da kuma lokacin kammala aikin

Jerin hanyoyi 25 da Buhari zai yi, kudin su da kuma lokacin kammala aikin

A kokarinta na sawwaka ma yan Najeriya wahalhalun dake tattare da bin hanyoyin Najeriya, musamman wadanda ke hade garuruwa, gwamnatin Najeriya ta himmatu wajen cigaba da ayyukan wasu manyan hanyoyi guda 25 a duk fadin kasar.

Gaba daya jimillan kudin da za'a kashe akan hanyoyin guda 25 ya tashi a naira biliyan 100.

Wasu daga cikin hanyoyin nan sun hada da gadar Oju/Loko-Oweto dake samar tafkin Benuwe ya isa har kauyen Loko dake Nassarawa akan farashi N144,708,134.18, kuma za’a kammala shi a watan Disambar 2017.

KU KARANTA: Rayuwar Mata a yankin Arewa na cike da ƙalubale masu tarin yawa – Inji Rahama Sadau

Aikin mayar da titin Abuja-Abaji-Lokoja tagwayen hanya, akan naira biliyan 3, kuma za’a kammala shi cikin watan Maris din 2018, kamar yadda NAIJ.com ta ruwaito.

3- Cigaba da mayar da titin Suleja-Minna tagwayen hanya, wanda za’a kashe masa naira 3,521,958,532,49, kuma a gama shi a watan Afrilun shekarar 2018.

4- Raba hanyar Abuja-Abaji-Lokoja, sashi na hudu daga katon karfe zuwa Lokoja akan kudi naira biliyan 3 da miliyan 500, inda ake sa ran kammala aikin a watan Janairun 2018.

5- Mayar da titin Lokoja zuwa Benin, faraway daga Obajana zuwa Okene, akan kudi naira biliyan 2 da miliyan 500, shima za’a kammala aikin a watan Janairun 2018.

Jerin hanyoyi 25 da Buhari zai yi, kudin su da kuma lokacin kammala aikin

Jerin hanyoyi

6- Rabar titin Kano-Maiduguri gida 2, wanda ya hade Kano-Jigawa-Bauchi-Yobe, akan naira 4,166,666,666.67, gamawa; Maris 2018.

7- Mayar da titin Kano-Maiduguri tagwayen hanyoyi, wanda ya hade Kano-Jigawa-Bauchi-Yobe da Borno, sashi na uku, daga Azare zuwa Potiskum, akan naira biliyan 3 da miliyan 5000, gamawa; Disambar 2017.

8- Gina tagwayen hanya akan titin Kano-Maiduguri sashi na hudu daga Potiskum zuwa Damaturu, akan naira biliyan 4, kuma a kammala aiki a watan Disambar 2017.

9- Gina tagwayen hanyoyi a kan hanyar Kano-Maiduguri, sashi na 4, daga Damaturu zuwa Maiduguri, za’a kammala aikin a watan Yuni 2017.

10- Gina tagwyen hanya Kano-Maiduguri, sashi an 1, daga Kano zuwa Wudi zuwa Shuari, akan kudi naira biliyan 5, gama aiki; watan Yunin 2018.

11- Tagwayen hanya Kano-Katsina, sashi na daya , daga Dawanau zuwa iyakar jihar Katsina, akan kudi naira biliyan 3, kuma za’a kammala aikin a watan Satumbar 2018.

12- Gina sabuwar babbar hanya a yammacin jihar Kano, sashi na 1, akan kudi naira biliyan 4, kuma za’a gama aikin a watan Mayun 2018.

13- Sabuwar babbar hanya a gabashin jihar Kaduna, da zata hade Kaduna da Abuja, akan kudi naira biliyan 4,666,666,6667, lokacin gama aiki: Janairun 2018.

14- Gyaran babbar hanyar data hade Onitsha zuwa Enugu, daga Amansea zuwa iyakar Enugu, akan kudi naira biliyan 5,166,666,666.67, a gama aikin a watan Disambar 2017.

15- Gyaran hanyar Enugu-Fatakwal, daga Lokpanta zuwa Umuahia, akan naira biliyan 4, kuma a gama aikin a watan Maris din 2018.

16- Gyarana hanya daga Enugu zuwa Fatakwal, sashi na 2, Umuahia zuwa Aba, akan kudi naira biliyan 3 da miliya 750, za’a gama aikin a watan Disambar 2017.

17- Gyaran hanya daga Enugu zuwa Fatakwal, sashi an 3, Enugu zuwa Lokpanta, akan kudi naira biliyan 3 da miliyan 750, a gama aikin a watan Disambar 2017.

18- Gyaran hanyar Enugu-Fatakwal, sashi an 4, daga Aba zuwa Fatakwal, akan kudi naira biliyan 3 da miliyan 500, a gama shi a watan Yulin 2018.

19- Gina tagwayen hanyoyi daga Yenegwe zuwa Kolo, zuwa Otuoke na jihar Bayelsa akan kudin naira biliyan 3 da miliyan 500, kuma a gama a watan Yulin 2018.

20- tagwayen hanya Lokoja-Benin, sashi na 1, daga Okene zuwa Auchi, akan kudi naira biliyan 3, a gama shi a watan Disambar 2017.

21- Tagwayen hanya Lokoja-Benin, sashi na 3, Auchi zuwa Ehor, akan kudi naira biliyan 3,166,666,666.67, za’a gama aikin a Yunin 2018.

22- Tagwayen hanya Lokoja-Benin, sashi na 4, cigaba da Ehor zuwa Benin, akan kudi naira biliyan 3 da miliyan 500, kuma a gama aikin a watan Disambar 2017.

23- Gyaran tagwayen hanyar Benin zuwa Ofosu-Ore-Ajebandele-Shagamu sashi na 4 akan kudi naira biliyan 6, kuma a gama shi a watan Disambar 2017.

24- Gyaran tagwayen hanyar Benin zuwa Ofosu-Ore-Ajebandele-Shagamu sashi na 3 akan kudi naira biliyan 5, za’a gama aikin a watan Disambar 2017.

25- Gina tagwayen hanya daga Ibadan-Ilori, sashi an 2, daga Oyo-hanyar Ogbomosho akan kudi naira biliyan 5 da miliyan 666, kuma a gama aikin a watan Disambar 2017.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.naij.com

Yan Najeriya sun koka da APC, kalla a NAIJ.com TV

Source: Hausa.naija.ng

Related news
A faɗa a cika: Minista Amaechi ya cika alƙawarin shigo da sabbin taragon jirgin kasa na zamani

A faɗa a cika: Minista Amaechi ya cika alƙawarin shigo da sabbin taragon jirgin kasa na zamani

Canji: Hotunan ƙarin sabbin taragon jirgin kasa na Abuja-Kaduna sun iso Najeriya
NAIJ.com
Mailfire view pixel