Victor Moses da Shehu Abdullahi sun shiga cikin jarumai goma sha daya na kungiyar CAF

Victor Moses da Shehu Abdullahi sun shiga cikin jarumai goma sha daya na kungiyar CAF

- Jaruman kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles biyu Victor Moses da Shehu Abdullahi sun yi nasarar shiga jerin jaruman yan kungiyar CAF guda goma sha daya

- Abdullahi ya lashe lambar yabo na jarumi a wasan da Super Eagles tayi da Zambia

- Najeriya tayi nasarar shiga sahun kasashen da za su buga gasar cin kofin duniya da za’a yi a Rasha a 2018

Kungiyar kwallon kafa ta Afrika (CAF) ta lissafo sunayen jaruman Super Eagles guda biyu Victor Moses da Shehu Abdullahi cikin mutane jarumai goma sha daya da suka yi nasarar shiga gasar cin kofin duniya.

Jaruma Super Eagles din guda biyu sun shiga jerin ne bayan kokari da suka yi a wasan da aka buga tsakanin Najeriya da Zambia a Uyo.

Victor Moses da Shehu Abdullahi sun shiga cikin jarumai goma sha daya na kungiyar CAF

Victor Moses da Shehu Abdullahi sun shiga cikin jarumai goma sha daya na kungiyar CAF

A baya NAIJ.com ta rahoto cewa Abdullahi ya lashe gasar jarumin wasa a wasar da sukayi da Zambia a Uyo sannan kuma an bashi naira miliyan daya da kuma buhun shinkafa goma.

KU KARANTA KUMA: Dan wasan Super Eagles Ahmed Musa ya zuba jari a gidan Mai da Gas

Dan wasan Liverpool Mohammed Salah ya shiga cikin jerin mutanen bayan rawar da ya taka wanda ya kai kasar Masar ga shiga gasar cin kofin duniya karo na farko tun 1990.

Har ila yau, dan wasa na kungiyar Chealsea, Victor Moses ya shiga jerin sunayen karo na uku a jere, bayan rawar da ya taka Super Eagles wacce ya kai ta ka shiga gasar cin kofin duniya.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwarzon ‘Yan wasan kwaikwayo Ali Nuhu na shirin lashe kyautar 2017

Gwarzon ‘Yan wasan kwaikwayo Ali Nuhu na shirin lashe kyautar 2017

Gwarzon ‘Yan wasan kwaikwayo Ali Nuhu na shirin lashe kyautar 2017
NAIJ.com
Mailfire view pixel