Rikicin NNPC: Baru ya zargi Kachiku da tunzura 'yan Najeriya

Rikicin NNPC: Baru ya zargi Kachiku da tunzura 'yan Najeriya

- Ana barota tsakanin shugaban NNPC da karamin ministan mai

- NUPENG da PENGASSAN sun koma bangaren Baru

- Biliyan 26 na dala ake zargin an salwantar a kwangila ta bogi

A karo na biyu, cikin kwanaki biyu, Maikanti Baru, shugaban kamfanin NNPC, wanda ke takun saqa da karamin ministan mai, kan zargin badakala da har ta zarta wadda a baya gwamnan babban banki murabus, Sunusi Lamido ya zargi Diezani Madueke da sacewa a baya.

Rikicin NNPC: Baru ya zargi Kachiku da tunzura 'yan Najeriya

Rikicin NNPC: Baru ya zargi Kachiku da tunzura 'yan Najeriya

Dakta Maikanti Baru din dai, ya ce kawai dai ministan na kokarin bata masa suna ne, da ma kuma neman tsugudidi wajen kunnen shugaba Buhari, ya kuma zargi Kachikun da kokarin lallai sai ya tunzura 'yan Najeriya da zantuka na karya.

Suma dai kungiyoyin kwadago na ma'aikatan man, NUPENG da PENGASSAN, a wata ziyarar kara kwarin gwiwa ga shugaban kanfanin, sun ce su suna goyon bayan Baru ne ba Kachiku ba. Hakan dai baya rasa nasaba da cewa ta hannunsa ne kawai mai ke fita ga 'yan kasuwa.

DUBA WANNAN: Shugaba Buhari na ganawar sirri da jami'an tsaro na kasa

A jawabin da yayi wa shuwagabannin na kungiyoyin, yace 'ina sane da yadda ake aikin nan, kuma ku ma kuna sane da yadda ayyuka ke tafiya, bab choge ba magu-magu', ya kara da fadi.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Dalilin da yasa kotu ta sake kekashewa akan bayar da belin Maryam Sanda

Dalilin da yasa kotu ta sake kekashewa akan bayar da belin Maryam Sanda

Dalilin da yasa kotu ta sake kekashewa akan bayar da belin Maryam Sanda
NAIJ.com
Mailfire view pixel