Gargadi na marmaza: Buhari ya janye dakarun soji daga Kudu maso Gabas - Wata kungiyar kare hakkin dan Adam

Gargadi na marmaza: Buhari ya janye dakarun soji daga Kudu maso Gabas - Wata kungiyar kare hakkin dan Adam

A ranar Litinin 9 ga watan Oktoba din da ta gabata, wata kungiyar kare hakkin bil Adama ta kasar Amurka mai sunan Rapid Response Fact-Finding Mission, RRFFM, ta umarci shugaban kasa Muhammadu Buhari akan ya janye dakarun soji daga yankin Kudu Maso Gabashin kasar nan dake aiwatar da gudanawarsu a yankin.

NAIJ.com ta ruwaito daga wata sanarwa daga birnin Washington na kasar Amurka da lauyan wannan kungiya reshen jihar Filato, Emmanuel Ogebe ya yi, inda ya ke cewa shugaban kasar Najeriya ya bayar da umarni ga dakarun sojin kasa akan su dakatar da gudanarwarsu a yankunan Kudu maso gabashin kasar nan har sai an bayyana dalilai da hujjoji da shari'a ta tanadar kuma take goyon bayan wannan gudanarwar.

Kungiyar ta na kara jaddada wannan gargadi, inda ta ce mafi dacewa shine a maishe da dakarun sojin yankin Arewa domin magance ta'addanci Boko Haram musamman iyakar kasar Nijar inda 'yan ta'addan Boko Haram suka kashe wasu dakarun soji hudu na kasar Amurka a makon da ya gabata.

A cewar kungiyar "Sojin kasan su dakatar da duk wata gudanarwarsu da take muzantanwa, tare da dakile hakkin bil Adama na yankin da kuma kai hare-hare da suke yi na gidan shugaban masu fafutikar ta neman kafa yankin Biyafara Kanu".

Gargadi na marmaza: Buhari ya janye dakarun soji daga Kudu maso Gabas - Wata kungiyar kare hakkin dan Adam

Gargadi na marmaza: Buhari ya janye dakarun soji daga Kudu maso Gabas - Wata kungiyar kare hakkin dan Adam

Kungiyar ta na kira ga dakarun sojin akan su bayyana adadin asarar da suka janyo a yankin sakamakon gudanarwar ta su. Sa'annan ta na kuma kara kira ga gwamnatin Najeriya akan ta bayar da dama domin cigaba da shari'ar Kanu a kotu a maimakon wannan cin kashi da sojin ta ke yi a yankunan.

KARANTA KUMA: Labarai cikin Hotuna: Matashi yayi fasahar kera jirgin sama a jihar Yobe

Ta kuma ce, "gwamnati ta yi azama cikin gaggawa wajen biyan diyya ga al'ummar da sojin ta janyo musu asarar rayukan 'yan uwansu da kuma dukiyoyi domin debe zargin ta'addanci akan su".

Domin shawara ko bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA

An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA

An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA
NAIJ.com
Mailfire view pixel