Amurka ta shirya kashe shugaban kasar Koriya ta Arewa, muhimman takardu sun nuna

Amurka ta shirya kashe shugaban kasar Koriya ta Arewa, muhimman takardu sun nuna

Masana ilimin kutse a yanar gizo sun bankaɗo wasu muhimman takardu daga kasar Koriya ka Kudu, wanda ke kunshe da sirrin karfon Sojan kasar, kamar yadda BBC ta ruwaito.

Majiyar NAIJ.com ta ruwaito cikin bayanan sirrin da aka bankado a cikin takardun, har da yadda kasar Koriya ta kudu tare da kawarta suka shirya yadda zasu kashe shugaban kasar Koriya ta Arewa, Kim Jong-Un.

Amurka ta shirya kashe shugaban kasar Koriya ta Arewa, muhimman takardu sun nuna

Shugaban kasar Koriya ta Arewa

Wani dan majalisar wakilan kasar Koriya ta kudu, Rhee Cheol-hee yace sun samu wannan bayanai ne daga ma’aikatar tsaron kasar, inda bayanan ke kunshe da matakan gaggawa da za’a dauka idan an fara yaki, tare da jerin kasashen kawance da kuma manyan kwamandojinsu na yaki.

KU KARANTA: Bana buƙatar izinin ka kafin na bada kwangila – Maikanti Baru ga Minsitan mai Kachikwu

Dan majalisa Rhee Cheol-hee yace tun a watan Satumbar bara ne suka gano kutse da kuma satan bayanai da kasar Koriya ta Arewa tayi a ma’aikatar tsaron Koriya ta kudu.

Sai dai kasar Koriya ta Arewa ta musanta wannan zargi, inda tace wannan irin karyar da Koriya ta kudu ta saba yi ne kawai, ba wani sabon abu bane.

An dai san kasar Koriya ta Arewa da kasar Koriya ta kudu tare da kasar Amurka a hannu daya basa ga maciji, inda kowa ke yin barazanar shafe kowa daga doron kasa, kuma wannan takaddama nada nasaba ne da shirin samar da makamin Nukiliya da kasar Koriya ta Arewa ke yi ne.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.naij.com

Source: Hausa.naija.ng

Related news
An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA

An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA

An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA
NAIJ.com
Mailfire view pixel