Ku bani shawara: Baturiya ta yi alkawarin bani miliyan 145 idan har na amince zan auri 'yar ta

Ku bani shawara: Baturiya ta yi alkawarin bani miliyan 145 idan har na amince zan auri 'yar ta

Wani dan Najeriya mai suna Johnny Creed yana neman shawarar 'yan Najeriya bayan da ya ce wata baturiya tayi alkawarin ba shi naira miliyan 145 matukar ya amince zai auri 'yar ta.

Wani matashin mayaki dan Najeriya mai suna Johnny Creed dan shekara 21 ya bayyana cewar wata baturiya ta amince zata bashi kudi matukar yayi alkawarin auren 'yar ta mai shekaru 18 a duniya.

Ku bani shawara: Baturiya ta yi alkawarin bani miliyan 145 idan har na amince zan auri 'yar ta

Ku bani shawara: Baturiya ta yi alkawarin bani miliyan 145 idan har na amince zan auri 'yar ta

Creed ya ce baturiyar ta furta masa hakan ne bayan da ya fada mata cewar bai taba soyayya da wata 'ya mace ba. Creed ya kara da cewar Baturiyar ta amince ta ba shi dala dubu 400, kwatankwacin naira miliyan 145 idan har ya yi alkawarin zai auri 'yarta ta duk da basu taba haduwa da ita 'yar ba.

DUBA WANNAN: Ku zargi Buhari da Shugabannin kabilar Igbo idan muka dauki maka dauki makamai domin yaki; In ji kungiyar IPOB

Creed dai ya ambata cewar ya shiga cikin rudani tun bayan jin wannan bukata ta baturiya domin yana ganin tamkar wani tarko ne ake so ya fada. A saboda haka ne ya garzayo yake neman shawarar 'yan Najeriya.

Wacce shawara zaku bawa wannan matashi?

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnatin Katsina za ta dauka malaman makarantun firamare 5,000

Gwamnatin Katsina za ta dauka malaman makarantun firamare 5,000

Gwamnatin Katsina za ta dauka malaman makarantun firamare 5,000
NAIJ.com
Mailfire view pixel