Shugabannin jam’iyyar PDP na Arewa suna kan ganawa da juna game da shugabancin jam’iyyar

Shugabannin jam’iyyar PDP na Arewa suna kan ganawa da juna game da shugabancin jam’iyyar

- Dattawan jam'yyar PDP reshen Arewa suna kan ganawa da juna a Abuja

- Fefesa Jerry Gana ke jagoranci taron shugabannin PDP na Arewa

- A watan disamaba ne jam'iyyar PDP za ta gudanar da zaben shugaban jam'iyya na kasa

Shugabanni da dattawan jam’iyyar PDP daga jihohin Arewa 19 suna kan ganawa da juna a babban birnin tarayya Abuja.

Tsohon ministar labaru da ala’adu Ferfesa Jerry Gana ya jagoranci taron.

NAIJ.com ta samu rahoton cewa shugabannin jam’iyyar PDP na Arewa za su tattauna matsalolin da jam’iyyar ke fuskanta da kuma zaben shugaban jam’iyya na kasa da za ayi a karshen wannan shekara.

Shugabannin jam’iyyar PDP na Arewa suna kan ganawa da juna game da shugabancin jam’iyyar

Shugabannin jam’iyyar PDP na Arewa suna kan ganawa da juna game da shugabancin jam’iyyar

A cikin wandada suka halarci taron akwai shugaban kwamtin rikon kwarya na jam’iyyar PDP, senata Ahmed Makarfi, yan majalissar dokoki na kasa da na jihohi, tsofaffin gwamnoni, da sauran su.

KU KARANTA : Buhari kamar cutar daji ne da ya kamata a kawo karshen shi – Fani Kayode

A watan disamba ne ake sa ran jam’iyyar PDP za ta gudanar da zaben shugaban jam’iyya na kasa wanda zai kawo karshen kwamitin rikon kwarya karkashin jagorancin senata Ahmed Makarfi.

A watan Satumba ne shugabannin jam’iyyar PDP reshen kudu maso gabas suka amince za su mara wa yankin Arewa baya wajen tsayar da dan takarar shugaban kasa zaben a zaben 2019.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Ashe Iran ke baiwa 'yan tawayen Yemen makaman yaki

Ashe Iran ke baiwa 'yan tawayen Yemen makaman yaki

Ta tabbata' Kasar Iran ke taimakawa 'yan tawayen Kasar Yemen
NAIJ.com
Mailfire view pixel