Dan wasan Super Eagles Ahmed Musa ya zuba jari a gidan Mai da Gas

Dan wasan Super Eagles Ahmed Musa ya zuba jari a gidan Mai da Gas

- Ahmed Musa ya bude wani gidan Mai da Gas a Kano

- Dan wasan gaban na Leicester City na kokarin habbaka kasuwancin sa

- Wannan sabon gidan man ya ci suna Mcya-7

Dan wasan Najeriya kuma dan gaban Leicester city Ahmed Musa na cigaba da habbaka birnin kasuwancin sa bayan ya budu wani gidan mai Myca-7 a yau, 10 ga watan Oktoba.

Tsohon dan wasan na Kano Pillars ya shigo Kano daga Abuja domin kaddamar da gidan man, bayan wani wasa a ranar Asabar, 7 ga watan Oktoba, a Uyo yayinda Najeriya ta samu wucewa gaba.

Jarumin ya je shafin sa na zumunta inda ya buga hoton sa rike da bututun mai a gidan man nasa.

Dan wasan Super Eagles Ahmed Musa ya zuba jari a gidan Mai da Gas

Dan wasan Super Eagles Ahmed Musa ya zuba jari a gidan Mai da Gas

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Buhari ya nemi yardan majalisar dokoki domin nemo rancen naira triliyan 2.3

A baya NAIJ.com ta rahoto cewa Ahmed Musa a gina wani katafaren wajen wasanni da motsa jiki a Hotoro GRA, Kano a farkon wannan shekara.

Wajen na da bangarori daban daban, wadanda suka hada da dakin shakatawa, gidan cin abinci da kuma babban dakin taro, sannan kuma an kaddamar da shi ne a ranar 15 ga watan Yunin 2017.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59

Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59

Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59
NAIJ.com
Mailfire view pixel