Yanzu Yanzu: Buhari ya nemi yardan majalisar dokoki domin nemo rancen naira triliyan 2.3

Yanzu Yanzu: Buhari ya nemi yardan majalisar dokoki domin nemo rancen naira triliyan 2.3

- Shugaban kasa Muhammadu Buhari na neman yarda domin nemo rancen wasu kudi yayinda Najeriya ke fafutukar ta

- An sanar da hakan ne ta hanyar wata wasika da aka aika majalisar dokoki

- Shugaban kasar na neman ranto dala biliyan 6.5 (naira triliyan 2.3) wanda za’ayi amfani da su wajen aiwatar da wasu ayyuka masu muhimmanci

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bukaci majalisar dattawan Najeriya da ta amince masa ya ciwo bashin dala biliyan 6.5 daga waje.

Shugaban kasar ya yi wannan roko ne ta hanyar wata wasika da ya aika ga shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki, da kuma kakakin majalisar wakilai, Yakubu Dogara.

Shugaba Buhari yace za ayi amfani da kudaden ne wajen biyan muhimman ayyukan da aka sa a kasafin kudin 2017 sannan kuma a biya wasu basussuka na cikin gida.

KU KARANTA KUMA: Badakalar NNPC: Shugaba Buhari yana tare da Baru; Kachikwu sai yayi a hankali

A take wasikar ya janyo hankalin sanata Phillip Aduda (PDP) wanda ke wakiltan babban birnin tarayya.

Sanatan wanda ya dasa aya, ya nemi abokan ayyukansa cewa a gayyato ministocin kudi da na kasafin kudi su zo su wayar dakai akan shirin fadar shugaban kasa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59

Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59

Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59
NAIJ.com
Mailfire view pixel