Zaben 2019: Tsohon gwamnan jihar Abia ya yi wata ganawar sirrance da IBB

Zaben 2019: Tsohon gwamnan jihar Abia ya yi wata ganawar sirrance da IBB

A ranar Litinin din da ta gabata ne, tsohon gwamnan jihar Abia Orji Uzor Kalu ya kaiwa tsohon shugaban kasar Najeriya na lokacin mulkin soja Ibrahim Badamasi Babangida ziyara, a gidan tsohon shugaban kasar dake birnin Minna na jihar Neja.

A yayin jawabai ga manema labarai bayan ganawar ta su ta sirrance, tsohon gwamnan ya bayyana cewa sun tattauna ne dangane da zaben shugaban kasa na 2019 mai gabatowa.

NAIJ.com ta ruwaito daga Kalu cewa, sun yi yarjejeniya kan cewa in har shugaban kasa Muhammadu Buhari ba zai sake tsayawa takara ba, to ya kamata Arewacin kasar nan ta yanke wanda zai maye gurbinsa domin har yanzu koron shugabancin Arewa ne.

Zaben 2019: Tsohon gwamnan jihar Abia ya yi ganawar sirrance da IBB

Zaben 2019: Tsohon gwamnan jihar Abia ya yi ganawar sirrance da IBB

Kalu ya kara da cewa, bayan Arewa ta kammala shugabancin kasar nan kuma, ya kamata a baiwa wasu yankunan damar su shugabanbci kasar nan a zaben shekarar 2023 domin hakan zai kara dankon zumunci da kuma hadin kan kasar wuri guda.

KARANTA KUMA: Rasha ta kera wani sabon Bam da ya yiwa makamin Nukiliya Fintinkau ta kowace fuska

Tsohon gwamnan ya sake jaddada bakansa na cewa, shugaban masu fafutikar neman kafa yankin Biyafara Nnamdi Kanu ya sulale zuwa kasar Landan daga kasar Malaysia.

Domin shawara ko bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
INEC ta kori jami'anta 2 akan zargin yi wa gwamnan jihar Kogi rajista so biyu

INEC ta kori jami'anta 2 akan zargin yi wa gwamnan jihar Kogi rajista so biyu

INEC ta kori wasu jami'anta 2 akan yi wa gwamna Bello rajista so biyu
NAIJ.com
Mailfire view pixel