Shugaban NNPC, Maikanti Baru ya sake caccakan Minista Kachikwu

Shugaban NNPC, Maikanti Baru ya sake caccakan Minista Kachikwu

- Maikanti Baru ya sake raddi ga ministan mai , Ibe Kachiwu

- Yace ministan ya kirkiro kudaden karya don tayar da hankalin jama'a ne kawai

Shugaban babban kamfanin man fetirun Najeriya, Dakt Kachalla Maikanti Baru, ya kuma caccakan karamin ministan man fetur, Ibe Kachikwu, akan zargin da yayi masa rashawa da rashin biyayya wanda ke kunshe cikin wasikar da ya turawa shugaba Muhammadu Buhari.

A wata raddi na biyu da yayu, Baru yace shi ba aikata wani laifi ba hakazalika bai saba wani doka ba. Yace Kachikwu bai da hurumin bada kwangila ko kuma hana bayarwa.

Shugaban NNPC, Maikanti Baru ya sake caccakan Minista Kachikwu

Shugaban NNPC, Maikanti Baru ya sake caccakan Minista Kachikwu

Mr. Baru yayi wannan bayani ne yayinda wasu manyan shugabannin kungiyoyin man fetur na PENGASSAN da NUPENG suka kawo masa ziyarar nuna goyon baya.

Ya tuhumci Kachikwu da kirkiran kudaden bogi domin kawai tayar da hankulan jama’an Najeriya kuma wannan abin kunya ne.

KU KARANTA: Kiwon Lafiya: Fa'idoji guda 9 na man ridi

Baru ya kara da cewa a matsayinsa na tsohon shugaban kwamitin yaki da rashawa na NNPC, ba zai yiwu ace shine zai saba wani doka ko od aba.

Yace: “ Na san wasu daga cikin ku wadanda ke bibiyan abubuwan da mukeyi kun san babu kudin da ya bace kuma babu dokan da aka saba.

Yadda muke bada kwangila daidai ne kuma zamu cigaba da hakan. Shugabannin basu da hurumin bada kwangila a NNPC,”.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Abin da Shugaba Buhari ya fadawa ‘Yan APC na Kasar Inyamurai a Villa

Abin da Shugaba Buhari ya fadawa ‘Yan APC na Kasar Inyamurai a Villa

Abin da Shugaba Buhari ya fadawa ‘Yan APC na Kasar Inyamurai a Villa
NAIJ.com
Mailfire view pixel