Buhari ne babbbar matsalar Najeriya – Reno Omokri

Buhari ne babbbar matsalar Najeriya – Reno Omokri

- Reno Omokri ya gudanar da zabe a tuwita game da matsalar da Najeriya ke fuskanta

- Mafi akasarin mutane sun zabe shugaba Buhari a matsayin matsalar Najeriya

- Fasto Omokri ya ce zaben da yan Najeriya suka yi, ya nuna Buhari bai cancnci shugabanci ba

Mai ba wa tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan Shawara a fanin watsa labaru Reno Omokri, yace shugaban kasa Muhammadu Buhari ne babbar matsalar da Najeriya ke fuskanta.

Omokri ya yanke wannan hukunci ne bayan zaben da ya gudanar a yanan gizo game da matsalolin da Najeriya ke fuskanta kafin zaben 2019.

Fasto Omokri wanda ya kasance mazaunin kasar Amurka, ya bayyana haka ne a shafin sa na tuwita.

Buhari ne babbbar matsalar Najeriya – Reno Omokri

Buhari ne babbbar matsalar Najeriya – Reno Omokri

A zaben da Omokri ya gudanar, ya tambayi yan Najeriya a shafin a na tuwita cewa, “Menen ra’ayin su game da matsalar da Najeriya ta fuskanata kafin zaben 2019."

KU KARANTA : Wata mata ta gurfana a gaban kotu bisa laifin sayar da jariri kan naira N605,000

Omokri ya ba da zabi hudu wanda ya kunshi:

1. Rashin aikin yi

2. Ta'adanci

3. Cin hanci da rashawa

4. Muhammadu Buhari

Mafi akasarin mutane a shafin sa, sun zabe shugaban kasa Muhammadu Buhari a matsayin matsalar da Najeriya ke fuskanta.

Omokri ya ce wannan kuri’o ya nuna Buhari bai cancanci shugabanci ba, kuma shine babbar matsalar da yan Najeriya suke fuskanta.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Dalilin da yasa kotu ta sake kekashewa akan bayar da belin Maryam Sanda

Dalilin da yasa kotu ta sake kekashewa akan bayar da belin Maryam Sanda

Dalilin da yasa kotu ta sake kekashewa akan bayar da belin Maryam Sanda
NAIJ.com
Mailfire view pixel