Buhari yaci amanar musulmai bisa nadin Aisha Ahmad a CBN

Buhari yaci amanar musulmai bisa nadin Aisha Ahmad a CBN

- Wani bawan Allah ya cacaki shugaba Buhari bisa nadin Aisha Ahmad a CBN ta kafar sada zumunta na Facebook

- Ya misalta shigar ta da irin na Karuwai saboda haka nadin da Buhari yayi mata cin fuska ne ga musulmi

- Daga karshe yayi nuni da cewa al’addun mu da ma dokar kasa basu amince da irin shigar da Aisha takeyi ba

Wani bawan Allah mai suna Abubakar Usman Almajiri yayi suka da kakausan murya bisa nadin da shugaba Muhammadu Buhari yayiwa Aisha Ahmad a matsayin mataimakiyar shugaban babban Bankin Najeriya wato CBN.

A cewarsa Buharin ya rasa musulmar da zai zabo face wadda ke shiga irin ta Karuwai wadda hakan babban cin fuska ne ga musulmin kasar nan.

Ya kara da cewa ya san cewa Buhari bai damu da kiyaye dokokin addinin musulunci ba musamman idan akayi la’akari da yadda yake musabaha da hanayen mata barkatai amma duk da hakan ya kamata ya zabo musulma ta gari ya bata wannan matsayin domin hakan ne zai sa al’umman musulmi suyi alfahari da ita.

Wani mutum yace Buhari yaci amanar musulmai bisa nadin Aisha Ahmad a CBN

Wani mutum yace Buhari yaci amanar musulmai bisa nadin Aisha Ahmad a CBN

Daga karshe yace ko da an ajiye maganan addini a gefe daya, ai akwai al’addun mu da sukayi nuni da saka sutura na mutunci har ma a dokan kasa akwai tsarin shiga na kamala da suturta jiki.

DUBA WANNAN: Kiwon Lafiya: Fa'idoji guda 9 na man ridi

Ga dai rubutun nasa a turance:

Wani mutum yace Buhari yaci mutuncin musulmai bisa nadin Aisha Ahmad a CBN

Wani mutum yace Buhari yaci mutuncin musulmai bisa nadin Aisha Ahmad a CBN

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Abin da Shugaba Buhari ya fadawa ‘Yan APC na Kasar Inyamurai a Villa

Abin da Shugaba Buhari ya fadawa ‘Yan APC na Kasar Inyamurai a Villa

Abin da Shugaba Buhari ya fadawa ‘Yan APC na Kasar Inyamurai a Villa
NAIJ.com
Mailfire view pixel