2019: Shugabannin PDP daga arewa suka yaudari Jonathan a 2015 – Inji Wike

2019: Shugabannin PDP daga arewa suka yaudari Jonathan a 2015 – Inji Wike

- Gwamnan jihar Ribas ya yi zargin cewa shugabannin PDP daga yankin arewa sun yaudari Goodluck Jonathan a 2015

- Wike ya ce PDP na tare da manyan tsoffofin shugabannin jam'iyyar da dama tare da wasu shugabannin APC

- Gwamnan ya zargi shugabannin PDP a arewa cewa sun hada baki a kan Jonathan

Gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas ya yi zargin cewa shugabannin PDP daga yankin arewa, ciki har da gwamnonin da ministoci, sun yiwa tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan munafurci a zaben 2015 wanda kuma ya ba Muhammadu Buhari damar zama shugaban kasa.

Ya ce jam'iyyar PDP tana tare da manyan tsoffofin shugabannin PDP da dama da kuma wasu shugabannin jam’iyyar mai mulki ta APC don yiwuwar samun nasara a shekara ta 2019.

Majiyar NAIJ.com ta tabbatar da cewar, Wike ya yi zargin cewa mambobin majalisar zartarwa na Jonathan a lokacin da yake mulki, da kuma manyan mambobin jam’iyyar PDP daga tsohon shugaban jam'iyyar, Adamu Mu'azu suka yaudari tsohon shugaban kuma suka gaya masa qarya a kan zai ci zabe.

2019: Shugabannin PDP daga arewa suka yaudari Jonathan a 2015 – Inji Wike

Gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas

KU KARANTA: Badakalar NNPC: Shugaba Buhari yana tare da Baru; Kachikwu sai yayi a hankali

Gwamnan ya caccaki shugabannin jam’iyyar na arewacin kasar, inda ya ce, "PDP a arewa sun hada baki a kan Jonathan. Bari a fadi gaskiya. Babu wanda zai mutu. Ba su gaya wa Janathan gaskiya ba”.

Sai dai ya ce kwamiti na sulhu na jam'iyyar PDP, wanda shi ne shugaban, cewa suna sa ran tattauna da tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo da kuma manyan mambobin APC, ciki har da tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar da Asiwaju Bola Ahmed Tinubu da sauransu.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59

Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59

Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59
NAIJ.com
Mailfire view pixel