Zaben 2019: A shirye muke mu sadaukar ran mu domin PDP tayi nasara - Gwamna Wike

Zaben 2019: A shirye muke mu sadaukar ran mu domin PDP tayi nasara - Gwamna Wike

- Gwamnan Jihar Rivers Nyesom Wike, ya ce a shirye suke wurin fuskantar zaben 2019 ko da ran su zai salwanta

- Ya ce PDP zata yi nasara a Jihar sa a zaben na 2019 kamar yadda tayi a 2015

- Ya ce za su lalamo 'yan APC zuwa PDP don tabbatar da sun ci zabe mai zuwa

Gwamnan Jihar Rivers Nyesom Wike, ya ce a shirye ya ke ya bada rayuwar sa don tabbatar da PDP ta yi nasara a zaben 2019 mai zuwa. Ya fadi hakan ne yayin tattaunawa da wata mujalla.

Wike ya ce Jonathan ya fadi zaben 2015 ne saboda yana kewaye da mutane marasa gaskiya musamman Ministoci. Ya kuma ce kamar yadda PDP ta yi nasara a Jihar Rivers a 2015, toh zanin ba zai canja ba a 2019.

Zaben 2019: A shirye muke mu sadaukar ran mu domin PDP tayi nasara - Gwamna Wike

Zaben 2019: A shirye muke mu sadaukar ran mu domin PDP tayi nasara - Gwamna Wike

Ya misalta Jonathan a matsayin mutumin kirki da dabi'u masu kya. Ya kuma ambaci tsabar hakurin Jonathan musamman lokacin da aka jefe shi yayin kamfen na zaben 2015, a inda wike ya ce in da shi ne kuwa sai dai Najeriya ta kone kurmus amma ba zai hakura ba.

DUBA WANNAN: Rikicin Baru da Kachikwu: Kungiyoyin ma'aikatan man fetur sun goyi bayan Baru

Gwamnan ya kuma yaba abun da Godsay Orubebe ya yi a zauren kirga kuri'un zaben 2015. Ya yi ikirarin magudin da aka tafka a zaben na 2015 a zahiri ya ke.

Wike ya ce idan ta kama za su lalamo tsaffin Gwamnonin Legas da Kano wato Tinubu da Kwankwaso don ganin sun yi nasara. Za kuma su lalamo wasu manyan 'yan siyasan da ba ma su din ba.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Source: Hausa.naija.ng

Related news
A faɗa a cika: Minista Amaechi ya cika alƙawarin shigo da sabbin taragon jirgin kasa na zamani

A faɗa a cika: Minista Amaechi ya cika alƙawarin shigo da sabbin taragon jirgin kasa na zamani

Canji: Hotunan ƙarin sabbin taragon jirgin kasa na Abuja-Kaduna sun iso Najeriya
NAIJ.com
Mailfire view pixel