Zaben 2019: Atiku ya fara kamfe a yankin Kudu maso Gabas

Zaben 2019: Atiku ya fara kamfe a yankin Kudu maso Gabas

- Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar zai fito takaran shugaban kasa a 2019, inji Ambasada Aliyu Bin Abbas

- Ya kuma ce har ya fara gangamin wayar da kawunan masu kada kuri'a a yankin Kudu maso Gabas na Kasan nan na jihar Anambra

- Ya kara da cewa talaka yana cikin ran Atiku a irin wannan yanayi na matsin tattalin arziki

A ranar Litini ne tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya fara wayar da kawunan masu kada kuri'a a Jihar Anambara yana mai shirya ma zaben shugaban kasa na 2019 mai zuwa.

Ambasada Aliyu Bin Abbas wanda shine Shugaban Kungiyar Atiku ta Tallafawa Gajiyayyu na Kasa, shi ne ga fadi cewan Atiku zai fito takaran. Ya fadi hakan ne yayin kaddamar da jami'an Kungiyar na reshen Anambara.

Zaben 2019: Atiku ya fara kamfe a yankin Kudu maso Gabas

Zaben 2019: Atiku ya fara kamfe a yankin Kudu maso Gabas

Abbas ya ce Atiku zai fito takaran ne don kawo chanji mai ma'ama cikin dukkan bangarorin tattalin arzikin kasan nan. Ya kuma ce Atiku ya kafa wannan kungiya ne saboda talaka na ran sa a irin wannan halin matsin tattalin arziki.

DUBA WANNAN: Zaben 2019: Atiku Abubakar da Jonathan sun yi ganawar sirri

Ya kara da cewa, Atiku ya hada gwiwa da wata kungiyar tallafi na kasashe don shigo da kaya na yawan kudi dalan Amurka miliyan 5.5 wadanda za'a rarraba ma gidan marayu da sauran su. Za kuma a kaddamar da kungiyar a sauran Jihohin Kasar nan.

Shi kuwa shugaban kungiyar reshen Anambara mai suna Ndubuisi Obijiofor cewa ya yi, ''Muna cikin babban matsala a Najeriya. Mun yi imani Atiku ne zai magance mana matsalar.''

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Source: Hausa.naija.ng

Related news
An fara samun sauki a gidajen man fetur da ke birnin tarayya, Abuja

An fara samun sauki a gidajen man fetur da ke birnin tarayya, Abuja

Layin man fetur da ta kuno kai a Abuja ta fara raguwa sosai a halin yanzu
NAIJ.com
Mailfire view pixel