Badakalar NNPC: Shugaba Buhari yana tare da Baru; Kachikwu sai yayi a hankali

Badakalar NNPC: Shugaba Buhari yana tare da Baru; Kachikwu sai yayi a hankali

- Bisa dukkan alamu Fadar Shugaban kasa na tare da Shugaban NNPC

- An dan samu takaddama tsakanin Ministan mai da Shugaban na NNPC

- Shugaban Kasa Buhari ya nemi Shugaban NNPC Baru ya wanke kan sa

Kamar dai yadda labari ke zuwa mana daga Jaridar The Nation bisa dukkan alamu Fadar Shugaban kasa na tare da Shugaban NNPC a rikicin su da karamin Ministan mai na kasar.

Badakalar NNPC: Shugaba Buhari yana tare da Baru; Kachikwu sai yayi a hankali

Shugaba Buhari ya nemi Baru ya wanke kan sa

Ministan mai na Kasar Ibe Kachikwu ya zargi Kamfanin NNPC da sabawa dokar kasa wajen bada wasu kwangiloli a kasar a wata wasika da ya aikawa Shugaban kasa Buhari. Sai dai tuni Shugaban kasar ya nemi Shugaban NNPC ya wanke kan sa kuma yayi jiya.

KU KARANTA: Shugaba Buhari ya sauka daga Ministan mai - Falana

NNPC ta bayyana cewa ba ta sabawa dokar kasa ba kuma Ibe Kachikwu a matsayin sa na karamin Ministan mai na kasar bai da hurumi wajen abin da ya shafi bada kwangilolin mai. Da alamu kuma NNPC ta gamsar da fadar Shugaban kasa bayan ta nuna mata shaida a fili.

KU KARANTA: Falana Shugaba Buhari ya sauka daga matsayin Minista

Ko da dai Shugaban kasar bai ce uffan ba wasu na ganin cewa akwai wata makarkashiya a takardar da karamin Ministan ya aikawa Shugaban kasar kuma yanzu haka dole ya bi a hankali domin gudun jawo abin da zai kawo wata matsala.

Majiyar mu tace Fadar Shugaban kasar dai bai ta yarda da maganganun Ministan na ta ba saboda zargin yayi yawa da ya zama gaskiya. Kwanaki dai Femi Fani-Kayode yace haka za ayi don Shugaba Buhari ya maida Inyamurai bayi a kasar nan.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Daukan dala ba gammo: Wani jami’in Soja ya ɗirka ma Mahauci harsashi a kan cin hancin N500

Daukan dala ba gammo: Wani jami’in Soja ya ɗirka ma Mahauci harsashi a kan cin hancin N500

Illar cin hanci: Sojan Najeriya ya bindige wani Mahauci a kan ya hana shi N500 na goro (Hoto)
NAIJ.com
Mailfire view pixel