Wasu magoya bayan shugaba Buhari sun bukaci yayi wa gwamnatin sa garambawul

Wasu magoya bayan shugaba Buhari sun bukaci yayi wa gwamnatin sa garambawul

Labaran da muke samu daga majiyoyin mu da dama dai na nuni ne da cewa har yanzu akwai da dama daga cikin magoya bayan shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari, dake ci gaba da kiransa akan yiwa gwamnatinsa garambawul da gyare-gyare duk don dai ya samu ya fita kunya ga kasar.

Daga daga cikin ire-iren su da majiyar mu ta tattauna da shi mai suna Haliru Sani Maiwa da ke zaman jigo a wata kungiya mai suna “Kungiyar Abokan Buhari” ya nuna rashin jin dadin sa bisa ganin cewa har yanzu yan PDP ne suka cika gwamnatin ta Buhari.

Wasu magoya bayan shugaba Buhari sun bukaci yayi wa gwamnatin sa garambawul

Wasu magoya bayan shugaba Buhari sun bukaci yayi wa gwamnatin sa garambawul

KU KARANTA: Yan majalisar Najeriya sun fi shugaban kasa albashi

NAIJ.com ta samu cewa a cewar dan gani-kasheni din na Shugaba Buhari, wadannan yan jam'iyyar PDP din dake a cikin Gwamnatin ta Buhari suna rike da mukamai kuma shugaban yaki ya fitar dasu a ganinsa su ne suke yiwa gwamnatin Buharin zagon kasa.

Da yawa daga cikin yan kasar dai sun yi tunanin cewa da Buhari ya dawo daga jinya a kasar Ingila a kwanan baya zai yi sauye-sauyen a gwamnatin sa amma har yanzu ba'aga yayi komai ba.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Dandalin Kannywood: Atiku ne kadai ke da mabudin gyaran Najeriya - Fati Muhammad

Dandalin Kannywood: Atiku ne kadai ke da mabudin gyaran Najeriya - Fati Muhammad

Dandalin Kannywood: Atiku ne kadai ke da mabudin gyaran Najeriya - Fati Muhammad
NAIJ.com
Mailfire view pixel