Dandalin Kannywood: Jaruma Umma Shehu ta kunyata a idon duniya

Dandalin Kannywood: Jaruma Umma Shehu ta kunyata a idon duniya

Fitacciyar jarumar nan ta fina-finan Hausa a masana'antar Kannywood ta kunyata a idon duniya a cikin wani shiri na Kundin Kannywood na gidan talabijin din Arewa 24 da yakan gayyato jarumai domin tattaunawa da su.

A cikin firar dai da Jarumi Aminu Shariff wanda aka fi sani da Momo da kuma ke zaman jagoran shirin yayi wa jaruma Umma Shehu tambaya ne game da bangaren musulunci inda ya tambayi jarumar ko wacece ta shayar da manzon Allah.

Dandalin Kannywood: Jaruma Umma Shehu ta kunyata a idon duniya

Dandalin Kannywood: Jaruma Umma Shehu ta kunyata a idon duniya

KU KARANTA: Atiku yayi ganawar sirri da Jonathan

NAIJ.com ta samu kuma dai cewa jin wannan tambayar ne ke da wuya sai jarumar hankalin ta ya tashi inda ta nuna rashin jin dadin ta game da lamarin har ta tambaye shi yaya zai yi mata haka duk da dai cikin dariya da raha.

Haka ma dai a cigaba da tsokacin da mutane ke ta yi game da lamarin, da dama sun soki Aminu Momo din da yi mata tambayoyin da ba su da alaka da wannan shiri yayin da kuma wasu ke ganin jarumar ta yi abin kunya na rashin amsa wannan tambaya.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shekara 5 kenan ko waya bai taba yi min ba - Mahaifin Mikel Obi ya tona asirin yadda dan nasa ya banzatar da shi

Mahaifin Mikel Obi ya tona asirin yadda dan nasa ya banzatar da shi, ya shekara 5 kenan rabonsu da ko waya

Shekara 5 kenan ko waya bai taba yi min ba - Mahaifin Mikel Obi ya tona asirin yadda dan nasa ya banzatar da shi
NAIJ.com
Mailfire view pixel