Abuja: Buhari ya gana da Tambuwal kan batun hako danyen mai a Sakkwato

Abuja: Buhari ya gana da Tambuwal kan batun hako danyen mai a Sakkwato

- Gwamnan jihar Sakkwato ya gana da shugaba Muhammadu Buhari a fadar gwamnatin tarayya da ke birnin Abuja

- Tambuwal ya yi ikirarin cewa akwai iskan gas da danyen man fetur makil a jiharsa

- Tambuwal ya yi jawabi ga shugaba Buhari a kan ziyarar samar da zaman lafiya da gwamnonin arewa 5 suka kai yankin kudu

Gwamnan jihar Sakkwato, Aminu Waziri Tambuwal ya gana da shugaban kasa Muhammadu Buhari a fadar gwamnatin tarayya da ke birnin Abuja domin tattauna batun aikin hako danyen mai a jihar Sakkwato.

NAIJ.com ta ruwaito cewa, Tambuwal yace akwai iskan gas da danyen man fetur makil a jiharsa wanda hakoshi zai bunkasa tattalin arzikin arewa da Najeriya baki daya.

Gwamnan ya kuma yi jawabi ga shugaba Buhari a kan ziyarar samar da zaman lafiya wanda gwamnonin arewa 5 suka kai a kudu maso gabas da kudu maso kudu.

Abuja: Buhari ya gana da Tambuwal kan batun hako danyen mai a Sakkwato

Gwamnan jihar Sakkwato, Aminu Waziri Tambuwal da shugaban kasa Muhammadu Buhari

KU KARANTA: Tinubu ya tsara abubuwa 7 wanda zai iya farfado da tattalin arzikin Najeriya

Tawagar wanda ta hada da Kashim Shettima na Borno da Aminu Masari na Katsina da Aminu Tambuwal na Sakkwato da Abubakar Bagudu na Kebbi da kuma Simon Lalong na Filato wanda suka yi a watan Satumban da ta gabata wanda kuma aka yi amfani da ita a matsayin sasantawa da inganta zaman lafiya da tattaunawa a dukkan bangarorin kasar.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Canji: Hotunan ƙarin sabbin taragon jirgin kasa na Abuja-Kaduna sun iso Najeriya

Canji: Hotunan ƙarin sabbin taragon jirgin kasa na Abuja-Kaduna sun iso Najeriya

Canji: Hotunan ƙarin sabbin taragon jirgin kasa na Abuja-Kaduna sun iso Najeriya
NAIJ.com
Mailfire view pixel