Gwamnatin Kano za ta bada horo na musamman na gyaran adaidaita sahu ga matasa 250

Gwamnatin Kano za ta bada horo na musamman na gyaran adaidaita sahu ga matasa 250

- Gwamnatin jihar Kano ta yi alkawarin horas da matasa 250 a kan gyaran adaidaita sahu a jihar

- Ganduje ya ce kungiyoyin adaidaita sahu zasu kawo mutane 150 inda gwamnati kuma za ta kawo mutane 100

- Gwamnati ta yi alkawari zata ba wadanda aka horas tallafin kayan gyara

Gwamnan jihar Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya karbi bakuncin kungiyoyi na masu gyaran adaidaita sahu da kuma tukawa a karkashin jagorancin mai bawa gwamna shawara a kan ababan hawa, Mallam Idris.

Gwamnan ya yabawa kungiyoyin a cikin jawabinsa bisa yadda suka rike sana'ar su hannu bibiyu, musamman ganin yadda tattalin arizikin kasar ta barbare a yanzu haka.

Ganduje ya yiwa kungiyoyin albishir da cewa gwamnatin jihar a karkashin jagorancinsa tare da hadin gwiwar kamfanin yin adaidaita sahu wato Bajaj zasu bada horo na musamman na gyaran adaidaita sahu ga mutane 250 a fadin jihar.

Gwamnatin Kano za ta bada horo na musamman na gyaran adaidaita sahu ga matasa 250

Gwamnan jihar Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje da kungiyoyin masu adaidaita sahu

Ya ce kungiyoyin zasu kawo mutane 150 inda gwamnati kuma za ta kawo mutane 100.

KU KARANTA: Gwamnatin Kaduna za ta dakatar da malaman makarantun firamare 20,000

Gwamnan ya ci gaba da cewa bayan kammala horon, gwamnati zata basu tallafin kayan gyara.

Haka zalika Gwamna Ganduje ya ce gwamnatin sa kwanan nan zata sai adaidaita sahu da kananan motoci na kurkura har da ma Bus domin inganta harkar sufuri a jihar.

A nasu jawabin, shugabbin kungoyin sum gode wa Gwamna Ganduje bisa wannan tallafi, sun kuma kara da cewa zai taimaka musu kwarai wajen inganta sana'ar su.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59

Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59

Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59
NAIJ.com
Mailfire view pixel